Abubuwa 5 da Buhari zai sa a ransa kafin ya ci zabe

  • Sani Aliyu
  • Multimedia Broadcast Journalist
Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Muhammadu Buhari ne dan takarar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya

A yayin da Najeriya ke shirin gudanar da zabukan 2019, ga wasu abubuwan da Shugaba Muhammadu Buhari ya kamata ya yi domin lashe zaben shekarar 2019.

Shekara fiye da uku bayan da 'yan Najeriya suka zabi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa, gwamnatinsa ta fuskanci kalubale da dama wajen sauke nauyin da ya rataya a kansa na shugabancin kasar.

Wasu 'yan Najeriya na korafin cewa har yanzu ba su ga canjin da jam'iyyar shugaban kasar ta APC ta yi wa 'yan kasar na sauya akalar siyasar kasar ba.

Wasu na ganin idan Shugaba Muhammadu Buhari na son lashe zaben shugaban kasa, kuma jam'iyyarsa ta sami nasara a zabukan da ke tafe to dole sai ya yi wasu abubuwa.

BBC ta samo abubuwa biyar da ta ke ganin ya kamata ya yi kafin zaben na 2019 bayan da ta gana da wasu masu nazarin siyasar Najeriya.

1. Tsaro - Boko Haram da IPOB da masu satar mutane

Sojojin Najeriya sun sami nasarori masu yawa a kan kungiyar Boko Haram, musamman ma a yankin dajin Sambisa.

Amma har yanzu akwai sauran rina a kaba - kungiyar ta ci gaba da kai hare-hare irin na sari ka noke.

A baya-bayan nan mayakan kungiyar sun yi wa dakarun sojin Najeriya kofar rago, inda har suka kashe gomman su.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masana na ganin akwai bukatar Buhari ya sake zage dantse a harkar tsaro

Matsalar tana damun 'yan kasar, amma da alama gwamnatin Buhari ta mayar da hankalinta kan wasu batutuwa kamar inganta tattalin arziki.

Akwai kuma matsalar 'yan awaren IPOB da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya da ke kokarin kafa kasar Biafra mai cin gashin kanta.

Bayan wannan kuma, akwai batun masu satar shanu da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

Wani farfesa a jami'ar Maiduguri mai suna Umar Pate ya ce 'Yan sanda da sauran jami'an tsaro na kasar "na bukatar kayan aiki da kulawa ta musamman domin su sami zarafin dakile ayyukan miyagun masu aikata manyan laifuka."

Ya kara da cewa "yana da muhimmanci Buhari da gwamnatinsa su dauki kwararan matakan da za su kawo karshen wadannan matsalolin kafin lokacin zaben."

2. Tattalin arziki musamman yaki da talauci a arewacin Najeriya

Batun tattalin arziki na cikin abubuwa uku da Shugaba Buhari ya dauki alkwarin magancewa a yayin yakin neman zabensa na 2015.

A lokacin Buhari ya koka da yadda ake canjin dalar Amurka daya a kan Naira 216, inda ya ce lamarin na lalata tattalin arzikin kasar.

Amma shekaru uku bayan ya dare kan karagar mulki, 'yan Najeriya na sauya dala daya ta Amurka da fiye da Naira 360.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu na ganin ana cikin tsananin wahalar rayuwa

Ban da wannan kuma akwai batun tsadar kayan masarufi da tsadar rayuwa, da suka addabi 'yan kasar.

Masu sharhi kamar Mahmud Jega na ganin akwai bukatar shugaban ya sake sabon lale kan wannan batun kafin lokacin zaben ya zo.

"Akwai batutuwan tsadar rayuwa da rashin kyawun hanyoyin sufuri da kan taimaka wajen kara tsadar kayan da ake samarwa a cikin kasar. Zai taimaka wa Buhari matuka idan aka mayar da hankali kan wadannan batutuwan".

3. Ci gaba da ayyukan da suka tsaya a sassan Najeriya

Ayyukan raya kasa a sassan Najeriya da gwamnatin Buhari ta gada daga waccan gwamnatin ta Goodluck Jonathan.

Akwai kuma wasu ayyukan da ita kanta ta soma aiwatarwa, kamar sabunta manyan hanoyin mota da samar da hanyoyin jiragen kasa.

Wadansu ayyukan sun hada da samar da ingantattun dakunan karatu a makarantu, da ciyar da daliban makaranta.

Asalin hoton, Presidency

Ban da wadannan ma akwai na samar da magunguna da kayayyakin aiki a asibitocin kasar, kamar yadda Farfesa Umar Pate ke kallon batun:

"Duk da cewa gwamnatin Buhari ta yi nasarar samar da hanyoyin jiragen kasa a wasu wurare, amma da bukatar ta inganta harkar sufuri ta hanyar gina wasu sabbin hanyoyin mota da samar da wasu gine-gine na zamani da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar."

4. Ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa

Yaki da cin hanci da rashawa na cikin manyan abubuwan da gwamnatin Buhari ta fi mayar da hankali a kai.

Amma rashin bin diddigin batutuwan cin hanci da rashawa da suka bayyana, da gazawa da wasu ke kallo na gwamnatin ta gurfanar da wasu da ake kallon shafaffu da mai ne na cikin abubuwan da gwamnatin Buhari ya kamata ta dauki mataki a kai gabanin zabukan 2019.

Mahmud Jega na ganin Muhammadu Buhari na gaban Atiku Abubakar a wannan fagen, sai dai ya ce da sauran aiki a gaban shugaban kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yaki da cin hanci da rashawa na cikin manyan abubuwan da gwamnatin Buhari ta fi mayar da hankali a kai

"Labaran da muka samu cewa an ki hukunta wasu jami'an wannan gwamnatin da ake tuhuma da aikata ba daidai ba na nuna zurfin matsalar. Dole ne Buhari ya fara daukan mataki a kan dukkan rahotanni irin wadannan."

5. Zawarcin masu zabe

Duk da cewa Buhari na da magoya bayansa a arewacin Najeriya da yankin kudu maso yammacin kasar, akwai wasu batutuwan da ya kamata ya lura da su.

Atiku Abubakar shi ne dan takarar jam'iyyar adawa wanda ya fito ne daga yankin arewacin kasar kamar Buhari, kuma babu shakka zai sami goyon bayan wasu daga cikin 'yan yankin wanda zai rage wa Buhari yawan magoya bayansa.

Akwai kuma matsalar wasu 'ya'yan jam'iyyar ta APC da suka fice saoda bambance-bambancen ra'ayin siyasa. A watannin baya, APC ta rasa gomman 'yan majalisar kasar wadanda yawancinsu sun koma jam'iyyar adawa ta PDP.

Asalin hoton, Getty Images

Mahmud Jega ya ce "Buhari na bukatar tabbatar wa magoya bayansa a arewacin kasar cewa bai manta da su ba, sannan kuma yana da jan aiki a gabansa wajen karkato da hankulan al'umomin kabilar Igbo da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya."

Ya kuma ce "Idan bai tashi tsaye ba wajen zawarcin masu zabe, da akwai yiwuwar dan takarar jam'iyyar PDP ya sami galaba a wasu yankunan kasar wanda ke iya zama masa gagarumin koma baya nan da lokacin zaben."