Shaidu a shari'ar Murtala Nyako sun yi mutuwar al'ajabi

Murtala Nyako
Image caption Murtala Nyako ya dade yana fuskantar zargin cin hanci

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta ce mutum biyu da suke bayar da shaida kan zargin da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Adamawa na damfarar da ta kai N29bn sun yi mutuwar al'ajabi.

Sanarwar da mai magana da yawun EFCC, Tony Orilade, ya fitar ta ce jami'inta mai suna Adekunle Odofin ya shaida wa alkalin kotun da ke sauraren karar cewa mutanen sun mutu ne jim kadan bayan sun bayar da shaida.

Ana zargin Murtala Nyako da Sanata Abdul-Aziz Nyako da Abubakar Aliyu da kuma Zulkifikk Abba da aikata laifuka 37 wadanda suka hada da sata da damfara.

Shaidun na da matukar muhimmanci a shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan na jihar Adamawa, in ji EFCC, a cikin bayanin da jami'inta ya yi wa alkali Okon Abang na wata babbar kotun Abuja ranar Talata.

EFCC ba ta yi karin haske kan abin da ya yi sanadin mutuwar shaidun ba.

Daga nan ne alkalin ya dage sauraren karar zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba, 2018 domin ci gaba da shari'ar.