Kwankwaso ya ce ya yi yunkurin hana fitar da bidiyon Ganduje

Kwankwaso da Ganduje Hakkin mallakar hoto KANO GOVERNMENT

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya ce ya yi yunkurin ganin ba a fitar da bidiyon da ya yi zargin nuna gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje yana karbar cin hanci daga wurin 'yan kwangila.

Dan majalisar dattawan ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan rediyon Dala FM da ke jihar ta Kano.

A cewar sa, "Kafin a fitar da bidiyon na samu labari, amma na ce kar su sake shi, saboda abin kunyar ba kawai na iyalin gwamna ba ne, abu ne da ya shafi martabar mutanen Kano da addininsu da kuma kujerar da na rike mai alheri."

Sanata Kwankwaso ya kara da cewa dukkan mutanen Kano sun zama abubuwan kyama a idanun duniya saboda abin da ake zargin gwamnan jihar da aikatawa.

Ya ce gwamna Ganduje masoyinsa ne wanda ya rikida ya koma makiyi.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya sha alwashin yin aiki tukuru wajen ganin an sauya "wannan gwamnati rubabbiya."

A watan jiya ne jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a shafin intanet ta fitar da jerin bidiyon da ya nuna Gwamna Ganduje yana cika aljihunansa da bandir-bandir na dalolin Amurka ta yi zargin cin hanci ne daga wurin 'yan kwangila.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce har ta kai ga majalisar lafa kwamitin da zai gudanar da bincike.

Mawallafin jaridar, Malam Jaafar Jaafar, wanda ya gurfana a gaban majalisar rataye da Alkur'ani mai tsarki, ya dage cewa bidiyon na gaske ne.

Sai dai wakilin gwamnan, kwamishinan watsa labaran jihar, Malam Garba Mohammed, ya ce bidiyon na karya ne.

Amma a karon farko gwamna Ganduje ya yi tsokaci kan batun inda ya ce yada bidiyon ba zai hana shi cin zabe a 2019 ba.

Ganduje ya ce wasu 'yan hamayya sun dogara wajen yada bidiyon zargin karbar kudaden a matsayin hanyar da za ta kai su ga cin zabe.

Labarai masu alaka