An rufe cibiyoyin da ke 'zubar da ciki' a Nijar

Taswirar Nijar

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun bayar da umarnin rufe cibiyoyi biyu na wata hukumar agaji ta Birtaniya, Marie Stopes International, inda suka ce suna ayyukan zubar da ciki ba bisa ka'ida ba.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya rawaito cewa ma'aikatar lafiyar kasar ta ce an dauki wannan mataki ne saboda bukatar hakan ta taso.

A shekarar 2006 ne, gwamnatin kasar ta Nijar ta zartar da dokar cewa ba za a zubar da cikin kowacce mace ba, har sai rayuwarta na cikin hadari sakamakon cikin da take dauke da shi.

Har ya zuwa yanzu dai kungiyar bata ce uffan ba a kan batun.

Kiyashi ya nuna cewa mace daya a Nijar na haihuwar 'ya'ya bakwai a tsawon rayuwarta, adadi mafi yawa a duniya.

A farkon wannan watan ne Kenya - wacce ita ma take da tsauraran dokoki kan zubar da ciki - ta ce ta dakatar da ayyukan zubar da ciki da kungiyar Marie Stopes International ke gudanarwa.

Labarai masu alaka