Sojojin Najeriya sun dakile harin 'yan Boko Haram

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Shugaba Muhammadu Buhari ke ziyarta jihar ta Borno ba Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Wannan dai ba shi ne karo na farko da Shugaba Muhammadu Buhari ke ziyarta jihar ta Borno ba

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun dakile harin da mayakan Boko Haram suka yi yunkurin kai wa a jihar Borno a ke arewacin kasar.

Sanarwar da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Talata da daddare ta ce 'yan ta'addar Boko Haram sun yi yunkurin kutsawa ta yankin Cross da ke karamar hukumar Kukawa.

Sai dai an yi nasarar dakile su, in ji rundunar sojin ta Najeriya.

Ba ta yi karin bayani kan yawan 'yan Boko Haram din da aka kashe lokacin gumurzun ba, tana mai cewa nan gaba kadan za ta yi cikakken bayani kan abin da ya faru.

Wannan yunkuri na kai hari na faruwa ne a yayin da ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Borno ranar Laraba.

A lokacin ziyarar tasa, shugaban zai gabatar da jawabi ga dakarun kasar da ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Ziyarar dai ta zo ne kwanaki kadan bayan 'yan Boko Haram sun kai munanan hare-hare da suka yi sanadiyyar rasa rayukan sojojin kasar kusan "100" a sansaninsu da ke jihar.

A tattaunawarsa da BBC mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari zai yi amfani da ziyarar wajen bude gagarumin taron ranar tunawa da sojoji wato 'Army day' da ake gudanarwa a kowacce shekara.

Garba Shehu ya kara da cewa ziyarar shugaban a wannan lokaci na da muhimmanci sosai domin ya gane wa idonsa yanayin da jihar ke ciki da kuma karbar cikakkun bayanai kan halin da ake ciki a yakin da dakarun kasar ke yi da Boko Haram daga shekara ta 2015 zuwa yanzu.

Kazalika Shugaba Buhari zai tattauna da sojojin da kwamandojinsu da ke filin daga da kuma ziyarta wadanda aka jikkata domin karfafa masu gwiwa, in ji Garba Shehu.

Malam Garba Shehu ya kuma musanta rade-radin da ake yi cewa watakila shugaban ya fuskanci rufa-rufa daga wurin kwamandojin da ke yakar Boko Haram a kan gaskiyar halin da ake ciki a yakin.

Labarai masu alaka