Abin da Shugaba Buhari ya ce a ziyarar Borno

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria Presidency
Image caption Shugaba Buhari lokacin da ya sauka a filin jirgin saman garin Maiduguri ranar Laraba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Borno a ranar Laraba.

A lokacin ziyarar tasa, shugaban ya gabatar da jawabi ga dakarun kasar da ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Ziyarar dai ta zo ne kwanaki kadan bayan 'yan Boko Haram sun kai munanan hare-hare da suka yi sanadiyyar rasa rayukan sojojin kasar kimanin "100" a sansaninsu da ke jihar.

Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria
Image caption Shugaban ya kai ziyara fadar Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai

Har ila yau shugaban ya kai ziyara fadar Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai.

Shugaba Buhari ya kuma ziyarci dakarun kasar da suka ji raunuka a mummunan harin da mayakan Boko Haram suka kai sansanin soji da ke garin Metale a karshen makon da ya gabata.

Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Buhari ya ziyarci dakarun kasar da suka ji raunuka a harin da mayakan Boko Haram suka kai sansanin soji da ke garin Metale

Sannan ya yi amfani da damar ziyarar inda ya yi wa sojojin kasar da ke bakin daga jawabi don ya kara musu karfin gwiwa kan aikin da suke yi.

Gabanin isar tasa Bornon, a tattaunawarsa da BBC mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya ce shugaban zai yi amfani da ziyarar wajen bude gagarumin taron ranar tunawa da sojoji wato "Army Day" da ake gudanarwa a kowacce shekara a kasar.

Tun da fari an shirya gudanar da taron ne a birnin benin na jihar Edo, amma daga bisani aka sauya zuwa jihar Borno.

Garba Shehu ya kara da cewa ziyarar shugaban a wannan lokaci na da muhimmanci sosai domin ya gane wa idonsa yanayin da jihar ke ciki da kuma karbar cikakkun bayanai kan halin da ake ciki a yakin da dakarun kasar ke yi da Boko Haram daga shekara ta 2015 zuwa yanzu.

  • Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar da muka yi da Garba Shehu kan ziyarar
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Muryar Malam Garba Shehu

Hakazalika Shugaba Buhari "zai tattauna da sojojin da kwamandojinsu da ke filin daga da kuma ziyarta wadanda aka jikkata domin karfafa masu gwiwa," in ji shi.

Daga nan, kakakin shugaban ya musanta rade-radin da ake yi cewa watakila shugaban ya fuskanci rufa-rufa daga wurin kwamandojin da ke yakar Boko Haram a kan gaskiyar halin da ake ciki a yakin.

Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria Presidency
Image caption A makon jiya Boko Haram ta kashe sojojin kasar kimanin '100' a garin Metele da ke jihar Borno

Labarai masu alaka