'Bugaggen likita' ya kashe mai jego da jaririnta yayin yi mata tiyata

Representational image Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matar da jaririnta sun mutu ne dan lokaci kadan bayan an yi mata tiyata

An kama wani likita a birnin Gujarar da ke yammacin Indiya saboda ya yi wa wata mata mai ciki tiyatar ciro jariri a lokacin da ya ke buge.

Ana kammala tiyatar jaririn ya mutu, yayin da ita kuma matar ta mutu jim kadan bayan aikin.

'Yan sanda sun tabbatar wa BBC faruwar lamarin, sun kuma bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa likitan a buge yake da giya.

Sai dai ana ci gaba da bincike kan ko mutuwar tana da dangantaka da sakaci ko kuma saboda wani dalili na lafiya.

Dr PJ Lakhani dai babban likita ne da ke da cikakkiyar kwarewa, sannan yana aiki ne a wani asibitin gwamnati tsawon shekara 15.

An kai mai nakudar Kamini Chachi asibiti ranar Litinin da yamma tana cikin tsananin ciwon nakuda.

Kafofin watsa labarai na cikin gida sun ce an shaidawa danginta da suke jira cewa, jaririn ya mutu, yayin da uwar kuma ke zubar da jini ba kakkautawa.

Dangin na ta sun yanke hukuncin mayar da ita wani asibiti mai zaman kansa, inda kuma ta mutu a hanya.

'Yan sanda sun shaidawa BBC cewa Dr. Lakhani ya kira su yana neman taimako, saboda yana tsoron cewa dangin na ta za su kai masa farmaki matukar su ka gano mutuwar matar.

Asibitin dai ya kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan dalilan mutuwar mai jegon da kuma dan na ta.

Labarai masu alaka