Kwana 23: Manyan abubuwa biyar da aka san Daura da su #BBCNigeria2019

daura

Garin yana cikin jihar Katsina ne a arewa maso yammacin Najeriya, kuma ya yi iyaka da Jamahuriyar Nijar ta wajen Damagaram daga arewa.

Sannan ya yi iyaka da jihar Jigawa ta Kazaure daga kudu.

Daura gari ne mai tsohon tarihi a kasar Hausa, kuma yawancin mazauna garin manoma ne. Masana suna ganin Daura ita ce asalin sarautar kasar Hausa.

Birnin Daura nan ne mahaifar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, kuma a can ne ya yi mafi yawan rayuwarsa.

A wannan makala, BBC ta yi duba kan manyan abubuwa biyar da Daura ta shahara da su, wadanda suka sa ta yi fice aka kuma san ta, ba a Najeriya kadai ba har da ma wasu sassan duniya baki daya.

Tarihi

Abu na farko da Daura ta yi zarra a fagensa shi ne tarihi. Babu yadda za a yi tarihin kasar Hausa ya kammala ba tare da an sako na Daura a ciki ba.

Rubuce-rubucen masana tarihi da dama sun nuna cewa Daura ita ce tushen Hausa da Hausawa, duk da cewa dai akwai masana da dama da ba su yarda da wannan hasashe ba.

Tana daga cikin manyan masarautun kasar Hausa da aka fi sani da Hausa Bakwai.

"Daura na da tasirin gaske ga kasar Hausa saboda al 'ummarta da al'adunta da ma yanayin zamantakewarta," kamar yadda Sulaiman Ibrahim Katsina ya ce.

Daura na da hamshakiyar masarauta wacce sarakuna daban-daban suka mulke ta tun daga zamanin Sarauniya Daurama har zuwa yau. An kuma san garin da tarihin kofofi da ganuwar gari da yawancin garuruwan kasar Hausa ke da shi.

Daurama

Idan dai za a yi magana kan garin Daura to dole ne a tabo batun Sarauniya Daurama, wacce ita ce Sarauniya mace ta karshe da ta mulki birnin.

Tarihi ya nuna cewa Daurama ita ce take sarauta a lokacin da Bayajidda ya iso garin ya kuma kashe macijiya sarki, sai ta aure shi saboda bajintarsa.

Daurama ita ce uwarsu Bawo wato ita ce uwar sarakunan Hausa Bakwai na Biram da Kano da Katsina da Zazzau da Gobir da kuma Rano.

Hakika duk wanda zai karanci tarihin kasar Hausa dole zai ci karo da na Sarauniya Daurama.

Image caption Ibrahim Isa a yayin da yake diban furarsa a birnin Daura a wata ziyara da ya taba kai wa

Bayajidda

Majiyoyi da dama sun yi amannar cewa ainihin Bayajidda daga Bagadaza ya zo, inda ya fara yada zango a Borno kafin daga bisani ya kaura zuwa Daura

A can ne ya samu wata takobi wanda da ita ne ya kashe wata macijiya da ta addabi mmutanen Daura a lokacin mulkin Daurama take hana su dibar ruwa a rijiya.

Daga bisani Daurama ta auri Bayajidda kuma shi ne "asalin Hausa da Hausawa" kamar yadda masana tarihi da dama suka bayyana. Amma wasu masana irin su Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) da Dr Abdallah Uba Adamu suna da ja kan wannan batu.

Kuna iya sauraron dalilan Farfesa Abdallah ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke kasa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Farfesa Abdallah Uba Adamu, shugaban Jami'ar Koyo daga Gida ta Najeriya

Kusugu

A lokacin da Bayajidda ya isa Daura a gajiye ya je, sai ya sauka gidan wata tsohuwa Ayyana. Ya bukaci ta sam masa ruwa ya sha, amma sai ta bayyana masa cewa babu ruwa don wata macijiya ke

hana su dibar ruwa sai Juma'a-Juma'a.

Bayajidda dai ya karbi guga ya tafi rijiyar ta Kusugu ya kashe macijiya ya sare kanta ya kuma debo ruwa. Bajintar tasa ce ta sa Sarauniya Daurama ta aure shi.

Rijiyar Kusugu na nan har yanzu a Daura, sai dai duk da cewa ba a dibar ruwa a cikinta, to ta zama wani kayan tarihi da mutane daga sassa daban-daban ke zuwa don ganin ta da kuma jin tarihinta.

Shi ya sa ma tarihin Daura ba ya cika sai da labarin Rijiyar Kusugu.

Manyan mutane

Baya ga al'amura na tarihi da suka wanzu shekaru da dama da suka gabata wadanda suka sa Daura ta yi fice a kasar Hausa da ma Najeriya baki daya, akwai kuma zaratan mutane da garin ya mallaka a wannan zamani da suka kara sa wa ya yi fice.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Janar Muhammadu Buhari tsohon shugaban kasar NAjeriya ne na mulkin soja kuma shugaban farar hula mai ci a yanzu, dan asalin garin Daura ne. A can aka haife shi kuma a can ya yi mafi yawan rayuwarsa.

Da wuya kuma ka samu mutumin da ya san Shugaba Buhari amma bai san cewa shi dan Daura bane, duba da yadda shugaban ke aiwatar da mai yawan al'amuransa a can.

Yana da gona da gida da kuma 'yan uwa da abokan arziki.

Mai martaba Faruk Umar Faruk, shi ne sarkin Daura mai ci a yanzu, kuma shi ne sarki na 60 a jerin ssarakunan masarautar, fitacce ne kuma shaharrre sosai a Najeriya musamman arewacin kasar.

Akwai Alhaji Usman Daurashi ne babban jami'in tsaro na Shugaba Shehu Shagari da Janaral Muhammad buhari da kuma JanarIbrahim Badamasi Babangida a zamanin mulkinsu, tun daga shekarar 1981-1989.

Sani Ahmed Daura shi ne gwamnan farko a jihar Yobe daga 1991 zuwa 1998

Sani Zangon Daura, Minsitan noma da raya karkara daga 1999 - 2000, sannan Ministan muhalli daga 2000 - 2001

Ja'afar Mahmud Adam, Fitaccen malamin addinin musulunci wanda ya yi mafi yawan rayuwarsa a Kano, amma mutane da dama sun san cewa shi dan Daura ne.

Lawal Musa Daura, ya rike mukamin shugaban hukumar tsaro ta farin kaya ta kasa, kuma an san shi sosai.

Hakkin mallakar hoto Presidency

Ambasada Mamman Daura tshohon jakadan Najeriya a Uganda da Saudiyya da Koriya Ta Kudu da Belgium da kuma Kamaru.

Sallar Gani

Bikin hawan sallar gani na daya daga cikin bukukuwan da masu sarauta da kuma dawaki ke kece raini a cikinsa, wanda kuma za a iya cewa ya samo asali a Daura, sannan garin ya yi fice wajen gudanar da wannan al'ada.

Masu gudanar da wannan biki dai sun ce biki ne mai tarihin gaske da ake yi tun zamanin Bayajidda wanda ke hada kan sarakunan kasar hausa a lokacin, amma bayan zuwan addinin musulunci sai aka yi masa kwaskwarima.

Alhaji Usman Yaro sarkin labaran masarautar Daura ya ce "sallar gani ta samo asali ne tun lokacin zuwan Bayajidda kasar Hausa, kalmar gani ta samo asali ne saboda duk lokacin da sarki ya shigo zai je ya sanar da mai martaba cewa gani na iso.

"Kuma an kirkireta ne domin gyara tafiyar da sha'anin mulki."

Mutane da dama dai kan halarci wannan biki na hawan sallar gani domin kashe kwarkwatar idanunsu.

Labarai masu alaka