Kotu ta daure shugaban UBE a Zamfara shekara 41

Shugaban hukumar UBE a Zamfara Murtala Adamu Jangebe Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Kotun daukaka kara ta yi watsi ne da hukuncin farko na Kotun tarayya a Gusau

Kotun daukaka kara a Sokoto ta yanke wa shugaban hukumar kula da karatun bai-daya UBE, a Zamfara Murtala Adamu Jangebe hukuncin daurin shekara 41 a gidan yari.

Mai shari'a Hannatu Sankey ce ta jagoranci zartar da hukuncin na alkalai biyar a kotun Sokoto, kamar yadda hukumar EFCC da ta shigar da karar ta tabbatar a wata sanarwa da kakakinta Tony Orilade ya aika wa BBC.

Kotun ta samu Jangebe da laifuka bakwai daga cikin 10 da kotun tarayya a garin Gusau na jihar Zamfara ta wanke shi tun da farko.

Kotun ta yi watsi da hukuncin farko ne da kotun tarayya a Gusau ta wanke Jangebe a watan Mayun 2017.

Kotun daukaka karar a Sokoto ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhume-tuhume guda bakwai daga cikin 10 da suka shafi halatta kudin haram da hukumr EFCC ta gabatar a kansa.

Kuma kan haka, a kan kowace tuhuma guda hudu kotun ta yanke masa hukuncin shekara biyar, sannan hukuncin daurin shekara bakwai ga duk sauran tuhume-tuhume guda uku.

Labarai masu alaka