Kun san makudan kudin da za a kashe a bikin Priyanka?

Priyanka da Nick Jones Hakkin mallakar hoto Business Today

A ranar 29 ga watan Nuwambar 2018 ne za a fara gagarumin bikin da jama'a da dama a fadin duniya suka jima suna jiran zuwansa.

Wannan bikin dai shi ne bikin jarumar fina-finan kasar Indiya Priyanka Chopra da Nick Jonas, wanda mawaki ne dan kasar Amurka.

Bikin zai fara kankama ne daga ranar biyu da uku ga watan Disamba.

Masoyan junan za su yi biki nau'i biyu, wato da na al'adar Hindu, wanda shi za a fara, sai kuma biki irin na kiristanci da za a yi washegari.

Za a shafe kwana biyar ana wannan kasaitaccen biki wanda za a yi shi a wani katafaren otel na Taj Umaid Bhawan da ke Jodhpur a kasar India.

Wannan otel dai na alfarma ne, domin sai wane da wane ke zuwa wajen, amma kuma rahotanni sun ce ma'auratan sun karbe kusan dukkan dakunan otel din saboda bakinsu masu zuwa wajen bikin.

Dangane da lissafin da aka yi na kudaden dakunan da aka kama a otel din, da abincin da za a ci da amfani da dakunan taron otel din da dai sauransu, an kiyasta cewa za a kashe kusan crore hudu a tsawon kwana biyar, kwatankwacin dala miliyan 60.

Wacece Priyanka?

Hakkin mallakar hoto YourStory

Fitacciyar jarumar fina-finan Bollywodd ce, tana daya daga cikin jaruman da ake biyan kudi mai tsoka a fim.

An haifeta a ranar 18 ga watan Yulin 1982.

Ta fara fim ne bayan ta samu nasara a gasar sarauniyar kyau ta duniya da aka yi a shekarar ta 2000.

Ta samu lambobin yabo da dama ciki har da kyautar jaruman da suka yi fice ta kasa, da kyautuka daga kamfanin filmfare.

Fim dinta na farko shi ne a Bollywood shi ne The Hero.

Tayi fina-finai da suka yi fice kamar Andaaz da Mujhse Shaadi Karogi da Aitraaz da Krrish da kuma Barfi.

Dangantaka tsakaninta da Nick Jonas

Hakkin mallakar hoto Vanity Fair
Image caption Priyanka da Nick Jonas

A watan Mayun da ya gabata ne masoyan junan suka bayyana wa duniya cewa suna soyayya.

Amma kuma tun a 2017, suka san juna har suke dan gaisawa.

Akwai dai tazarar shekaru a tsakanin Priyanka da Nick Jonas, inda ita ta bashi ratar shekara tara, ita yanzu haka tana da shekara 36, shi kuma 27.

To amma hausawa kan ce so baya hana ganin shekaru.

Labarai masu alaka