Gobara ta kone shaguna 200 a kasuwar Kamaru

gobarar kasuwar Kamaru

Kusan shaguna ne suka kone kurmus sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar kayan abinci a birnin Bamenda da ke yankin renon Ingila na kasar Kamaru

Gobarar ta tashi ne a ranar Alhamis, sai dai har zuwa yanzu kuma ba a san hakikanin abin da ya haddasa wannan gobarar ba.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakken rahoton Muhamman Babalala:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Rahoton Babalala kan gobarar Kamaru

Wata 'yar kasuwar ta ce abin da ta yi asara anan zai haura miliyan bakwai na CFA, sa'annan kuma ma akwai kayan da ta dauka a bashi da ba ta karasa biya ba.

Abubuwan da suke kunshe a cikin shagonta sun hada da buhunhunan shinkafa, akwai kwalayen kifin da a ranar Laraba ne ma ta shigo da su cikin kanti bayan dawowarta daga kauye wanda ta sayi ko wani kwali a kan jaka 70 wani 75.

Akwai buhunhunan filawa da tarin wasu kayan abinci da ba za ta iya bayyanawa ba. Babu wani abinda ya rage a cikin shagon kamar yadda ta shaida wa BBC.

Duk da kai daukin da 'yan kwana-kwana suka kai kasuwar, lamarin bai fi karfinsu ba, amma kuma wuri ya cakude da wuta.

Wani dan kwana-kwana ya ce sun yi kokarin gaggautawa domin shawo kan wutar, da takaita asarar da hakan ka iya haddasawa.

A yanzu dai ba za su iya bayyana wani sakamako ba, saboda suna ci gaba da gudanar da bincike. Sai dai ya ce lokacin da suka shiga kasuwar 'yan gadi sun ce musu wutar ta fara kunno kai ne a cikin shago guda.

Sau uku kenan a cikin shekaru biyu, wani sashe na kasuwar kayan abinci na birnin Bamenda yake konewa.

Gobarar baya-bayanan itace na watan Janairun shekaran a lokacin da aiki na kud-da kud tsakanin 'yan kwana-kwana da jama'a ya sa aka samu kashe wutar.

Gwamnati ta zargi 'yan awaren kasar da ke neman ballewa daga Kamaru kan gobarar a wancan lokacin.

'Yan awaren dai suna kukan cewa ana nuna musu wariya kuma sun gaji da zama karkashin ikon kasar da Shugaba mai jin Faransanci Paul Biya ya shafe shakara 35 yana mulkarta.

Gwamnati tana zargin 'yan aware da zama "yan ta'adda" masu yi wa zaman lafiya da hadin kan kasar barazana.

Labarai masu alaka