Amurka za ta daina taimaka wa Saudiyya a yakin Yemen – Sanatocin Amurka

A child suffering from malnutrition in war-ravaged Yemen, 21 November Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al'ummar Yemen suna cikin matsanancin hali saboda yaki

Majalisar dattawan Amurka ta bijiro da wani kudiri da zai dakatar da taimakon da kasar take bai wa kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen.

Galibin sanatocin kasar ba su ji dadin kalaman Shugaba Donald Trump ba game da kisan dan jarida nan, Jamal Khashoggi.

Sakateren harkokin wajen kasar Mike Pompeo da kuma Sakataren tsaron kasar Jim Mattis sun bukaci sanatocin da kada su goyi bayan kudirin, inda suka ce hakan zai kara sa al'amura su tabarbare a Yemen.

Sanatoci 63 ne suke goyon bayan kudirin, yayin da 37 ba sa goyon bayansa.

Me ya sa sanatocin ba su ji dadin kalaman Trump ba?

An ci gaba da sukar kasar Saudiyya tun bayan kisan dan jarida Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya a ranar 2 ga watan Oktoba.

Hukumar leken asirin Amurka CIA ta ce Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ne ya ba da umarnin kisan dan jaridar.

Sai dai Shugaba Trump ya yi watsi da rahoton hukumar CIA.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Trump ya ci gaba da cewa batun ba zai shafi huldar kasuwanci da ta soji da ke tsakainsu da Saudiyya

Ya bayyana cewa dangantaka da Saudiyya tana da muhimmanci, kuma ya yi biris da kiraye-kirayen da ke cewa ya kamata a sanya wa shugabannin Saudiyya takunkumi.

Har ila yau, sanatocin sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda Shugabar hukumar CIA Gina Haspel ta ki halartar wani zama na musamman da majalisar dokokin kasar ta yi kan dangantakar kasar da Saudiyya a ranar Laraba.

"Lokaci da ya yi da za aike wa Saudiyya wani sako, kan keta hakkin dan Adam da mummunan halin da ake ciki a kasar Yemen," in ji Sanata Bob Menendez na jam'iyyar Democrat.

Mene ne tasirin wannan kudirin?

Nasarar da wannan kudin ya samu na nufin za a ci gaba da tattauna batun goyon bayan da Amurka take ba Saudiyya a mako mai zuwa.

Wasu sanatocin wadanda suke goyon bayan yakin Yemen, sun nuna goyon bayansu ga kudirin ne saboda nuna rashin amincewa da matakin gwamnatin Trump kan kisan Khashoggi.

Idan majalisar dattawan ta mayar da kudirin doka, wanda da wuya ya samu amincewar majalisar wakilan kasar, inda 'yan jam'iyyar Republican ne ke da rinjaye.

Kuma sun ki amincewa da irin wadannan kudirori a baya.

Amma kuma wannan zai iya sauyawa saboda a sabuwar shekarar nan ne, 'yan jam'iyyar adawa ta Democrat za su karfe iko da majalisar wakilan kasar.

Labarai masu alaka