Makahon da ke gyara wa masu ido keken dinki
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kun taba ganin Makahon da ke gyara wa masu ido keken dinki?

Muhammad Sani Dando ya gamu da laruran makanta tun yana yaro.

Amma duk da haka yana dinki da kuma gyaran keken dinkin. BBC ta tattauna da shi kan baiwar da yake da ita.

Ba kasafai ake samun makafi da basirar yin wasu abubuwa da sai mai ido ne ya ke yi ba.

Muhammad Sani ya ce ba zai yi bara ba, domin bara mutuwar zuciya ce.

Bidiyo: Yusuf Yakasai/Fatima Othman

Labarai masu alaka