Sarauniyar kyau ta Rasha ta Musulunta, ta auri Sarkin Malaysia

Oksana Voevodina Hakkin mallakar hoto Kualar Lumpur reporter

Wata tsohuwar sarauniyar kyau ta Rasha ta zama sabuwar Sarauniyar Malaysiya bayan da ta musulunta ta kuma auri sarki kasar Muhammad V na Kelantan.

Oksana Voevodina mai shekara 25 matashiya ce da mijin nata ya girme ta da shekara 24, wanda yake kan mulki tun shekarar 2016.

An yi bikin Voevodina da sarkin ne a birnin Moscow a wani biki na kasaita ranar 22 ga watan Nuwamba, kamar yadda jaridar New York Post ta ruwiato.

A wajen bikin dai ba sha barasa ba kuma ba a ci wani abinci da musulunci ya haramta ba.

Kafin ta zama matar sarki amaryar ta ce: "A lokacin da nake makaranta ni mara ji ce. Ina son masu hatsabiban maza masu wasan zamiya da masu wasan keke da manyan baburan tsere wadanda suje shiga gasa."

Amma daga baya ta yi tsokaci cewa: "Ina ga namiji ne ya kamata ya zama shugaba a gidansa kuma ya kamata samun sa ya fi na matar."

Ba a san Voevodina sosai ba baya ga ficen da ta yi a zaben Saruaniyar kyau ta Rasha a shekarar 2015.

Hakkin mallakar hoto Kuala Lumpur reporter

Ba a bayyana yadda ma'auratan suka hadu ba sannan babu tabbas kan ko ta taba aure kafin wannan.

Voevodina na da shekara 22 a lokacin da ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Rasha.

Mahaifinta Andrey Gorbatenko babban likitan kashi ne a wani asibiti da ke kudancin Rasha.

Ta ce ta gano sirrin kyawunta ne a lokacin da take makaramtar gaba da sakandare.

"Na fi kowa tsayi da siranta a ajinmu don haka sai na dinga damuwa. Amma shiga ta babbar makaranta ya sa na gane hakan abu ne mai kyau a gare ni." in ji ta.

Voevodina dai ta zabi sunan Rihana a matsayin sabon sunanta na musulunci.

Hakkin mallakar hoto New York Post

Labarai masu alaka