'Yan sanda sun kashe 'barayin shanu' 100 a Zamfara

'Yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar 'yan sandan ta ce ta kashe barayin shanu da dama

'Yan sandan Najeriya sun ce sun kashe 'yan ta'adda 104 a jihar Zamfara bayan wata fafatawa da suka yi a karamar hukumar Birnin Magaji, sannan kuma suka lalata maboyar 'yan fashin da dama.

Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar ta ce jami'an tsaron sun kuma rusa sansanoni uku na barayin, sannan suka kwato shanu sama da 500 da wasu dabbobi da dama.

Rundunar 'yan sandan ta ce an kashe dan sandanta daya yayin kwantar baunar da aka yi musu, sai dai wasu majiyoyin gwamnatin jihar sun shaida wa BBC cewa an kashe 'yan sanda da dama.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin Alhamis din nan, yayin da jami'an 'yan sanda na musamman ke sintiri a cikin dazuzzukan jihar ta Zamfara domin zakulo barayin shanu da masu garkuwa da mutane dake addabar sassan jihar da dama.

Haka kuma dakarun na musamman sun kama sama da mutum 85 da ake zargin gungun masu aikata miyagun laifuka ne a jihar.

Sanarwar ta ce an kuma kwato bindigogi kusan 80 da kuma wasu muggan makamai.

Sakamakon kwanton baunar dai rundunar 'yan sandan kasar ta tura babban mataimakin sufeto janar domin zama babban kwamandan dakarun na musamman.

Babban aikin kwamandan shi ne maido da zaman lafiya a duka fadin Zamfara.

Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu

Sharhi kan tarihin rikice-rikice a Zamfara - Daga Kadariyya Ahmed

Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar Zamfara.

A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala'i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar 'yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.

Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan 'yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.

Image caption Ana zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris ke ci gaba da aikata fashi

Hakan ta sa kauyukan da ke fama da matsalar barayin shanu da 'yan kato da gora suka fara kokarin ganin sunkare kansu da duk abun da ya kamata.

Daga haka sai rikicin ya kara ruruwa ta hanyar kai hare-hare da daukar fansa. A haka sai a ka kasa cimma kokarin shirin yin afuwa da aka so gabatarwa.

A yanzu dai muna ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansa ba.

Abun da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka