Matar da ta 'damfari' mutane a fadar Shugaba Buhari

Matar da ake zargin tana yi wa Aisha Buhari sojan gona Hakkin mallakar hoto DSS facebook
Image caption Ana zargin matar da damfarar wani dan kasuwa naira miliyan 150

Hukumar tsaro farin kaya ta DSS a Najeriya ta gabatar da wata mata mai suna Amina Mohammmed a gaban 'yan jarida a kan zargin amfani da fadar shugaban kasar domin damfarar mutane.

DSS ta ce matar tana shiga cikin fadar shugaban kasa ba tare da izini ba.

A cewar hukumar, matar ta rika yi wa wasu manyan jami'an gwamnati sojan-gona -- ciki har da matar gwamnan jihar Kogi.

Kakakin hukumar tsaro ta farin kaya, Peter Afunaya, ya ce matar ta rika shiga cikin gidan matar shugaban kasa Aisha Buhari.

Ya kuma ce ta rika amfani da sunaye daban-daban domin shiga cikin fadar shugaban kasar.

Sai dai kakakin DSS ya ce ana zargin matar da damfarar wani dan kasuwa naira miliyan 150 a shekarar 2017.

Ya ce ta rika amfani da sunan Aisha Buhari wajen damfarar mutane masu neman kwangila a fadar shugaban kasa.

Lamarin na zuwa ne bayan watanni uku da Hajiya Aisha Buhari ta zargi wani jami'in da ke kula da tsaron lafiyarta da amfani da sunanta wajen karbar makudan kudade daga wurin mutanen da ke neman alfarma a fadar shugaban kasa.

Hakkin mallakar hoto DSS facebook
Image caption Ana zargin matar da yi wa Aisha Buhari sojan gona

Sai dai jami'in dan sandan ya musanta zargin.

Labarai masu alaka