Kwana 24: Za ku zabi wanda limaminku ya ce ku zaba? #BBCNigeria2019

Bayanan bidiyo,

Kalli bidiyon ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya kan ko za su zabi wanda limaminsu ya ce su zaba

#BBCNigeria2019

Zaben 2019 na kara gabatowa kuma kamfen din siyasa na ci gaba da gudana a tsakanin sababbi da tsofaffin jam'iyyu.

Kusan kowane lungu da sako ka shiga za ka tarar maganar da ake kenan, daga teburin mai shayi zuwa shagunan kasuwanni.

A lokuta da yawa hakan yana tsallakawa ya tafi masallatan Juma'a da majami'u inda malaman addini ke shiga gaba wajen bayar da gudunmawarsu ta hanyoyin da suke ganin zai taimaki mabiya addinansu.

Tare da cewa muryoyin jagororin addini na da karfi wajen mahangar mabiyansu ta fuskar siyasa amma wasu lokutan ana zargin cewa wasu daga malaman na amfani da addinin ba ta hanyoyin da suka dace ba.

Asalin hoton, Aliyu Facebook

Bayanan hoto,

Aliyu matashi ne mai nazari kan fannoni daban-daban a Najeriya

Maimakon su zamo masu kare muradu da hakkokin mabiyansu baki daya sai wasu daga gurbatattun 'yan siyasa su yi amfani da muryoyinsu wajen juya akalar muradinsu daga taimakon talaka zuwa amfani da talakan ta hanyoyin da ba su dace ba.

Wannan ya janyo wasu daga mabiyan su na bijirewa zabin malaman nasu.

Tare da cewa kabilanci da bangarenci na taka muhimmiyar rawa wajen rayuwar 'yan Najeriya, to amma addini ya fi tasiri a mahangar 'yan kasar idan aka yi la'akari da cewa Najeriya tana da kabilu sama da 300 amma kabilun da suka fi tasiri ba su wuce guda uku da suka hada da Hausa-Fulani, Ibo da Yoruba ba.

Asalin hoton, Getty Images

Masana ilimin zaman jama'a na ganin cewa babu abin da yake da karfin tabbatar da alaka tsakanin mabanbantan mutane fiye da addini. Wannan ta sanya addini yake da tasiri wajen juya al'ummar da ta kasa juyuwa ko ta hanya mai kyau ko mara kyau.

Najeriya ita ce kasa mafi yawan mutane a nahiyar Afirka da mutum miliyan 182 a shekarar 2015.

Giwar Afrika, kamar yadda ake mata take, ta rabu gida biyu tsakanin Kudu mai yawan mabiya addinin Kirista da kuma Arewa mai yawan mabiya addinin Islama.

A tsakaninsu akwai mabiya addinin gargajiya kadan da ba su da ta cewa a siyasar kasar da ta cakude da kabilanci, bangarenci da kuma rarrabuwar kan mabiya addinai.

Har ya zuwa yanzu dai ba a da tabbacin kididdigar yawan Musulmi da na Kirista a Kasar, amma dai iya abin da aka iya ganowa ya nuna Musulmi sun fi Kirista yawa da kaso kadan.

Su kam mabiya addinin gargajiya ba su fi a kididdige cikin karamin lokaci ba. 'Yan tsirarun da ba sa bin addini kuwa ba su kai yawan da har sai an tsaya dogon lissafi a kansu ba.

A Najeriya da aka tabbatar da cewa tana daga cikin manyan kasashen da ake bin addini sau-da-kafa, malaman addini na Islama da na Kiristanci suna da matukar tasiri wajen juya akalar 'yan kasar.

Asalin hoton, Getty Images

A wasu lokutan malaman addini suna kokari su bayyana cewa kokarinsu na zabar ko kin zabar wani dan takara yana da alaka da hidimar addini ta hanyar daukaka ko kariya.

Wani abu da yake karawa mabiya armashin mika wuyansu ga malaman addini domin zabin siyasa shi ne tsoro da fargabar da take cikin rayukan wasu na cewa addininsu yana cikin hadari matukar suka zabi wani ba dan cikinsu ba.

Babban misali a nan shi ne, shekarun baya jama'ar kudancin Najeriya sun ta ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari na shirin kafa shari'ar Musulinci ne a kasar.

Wannan farfaganda ta sanya dole Buhari ya dinga dauko manyan malamai mabiya addinin Kiristanci domin su zamar masa mataimaka.

A wasu bangarorin kuma, da yawan malaman addinai suna kokari wajen ilimantar da mabiyansu kan harkokin zabe da kuma zaben shugabanni na gari.

Tamkar shugabannin gargajiya, ana ganin malaman addini a matsayin iyayen al'umma da suke haskawa mutane wadanda za su jagorancesu a lokutan zabe.

Malaman addinai na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da an yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana hade da addu'o'in wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Akwai manyan malaman addinan Islama da na Kirista da za su iya tasiri a zaben da ke karatowa na 2019, musamman a arewacin Najeriya.

Malaman na da mabiya masu yawa a fadin Najeriya da suke sauraron muryarsu har ta zamo mai tasiri ga mahangarsu. Manya daga cikinsu da muryarsu ke yawan fitowa sun hada da:

Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Asalin hoton, SHEIKH DAHIRU BAUCHI

Bayanan hoto,

Malamin, a matsayinsa na jagoran kungiyar da take da miliyoyin mabiya, ya kan shiga lamarin gwamnati ta hanyar kawo gyara ko suka a wasu lokutan

Dattijo ne kuma jagora ga mabiya darikar Tijjaniya a fadin Najeriya.

Tare da cewa tsufa ya kama shi amma har yanzu muryarsa na garawa a fanni daban-daban na rayuwar musulmin kasar, musamman 'yan darikarsa ta Tijjaniyya.

Duk da cewa har ya zuwa yanzu bai bayyana goyon bayansa ga wani dan takara ba amma ya umarci mabiyansa a lokacin bikin maulidin Sheikh Ibrahim Inyass da aka yi a Abuja a ranar Asabar 14 ga Afrilun 2018, da su yi rijistar zabe don su zabi shugabanni nagari a zaben 2019 da yake gabatowa.

Malamin, a matsayinsa na jagoran kungiyar da take da miliyoyin mabiya, ya kan shiga lamarin gwamnati ta hanyar kawo gyara ko suka a wasu lokutan.

Dr. Ahmad Abubakar Gumi

Malami ne da yake kan kujerar mahaifinsa Sheikh Abubakar Gumi. Tsohon soja ne kuma likita da ya yi karatun addinin Islama a kasar Saudiyya.

Asalin hoton, Dr Gumi Facebook

Bayanan hoto,

Ana ganin Dr Gumi a mai yawan sukar gwamnatin Buhari

An san malamin da sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fuskoki da dama. A 'yan kwanakin nan ya nemi gwamnati da ta saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky kamar yadda kotu ta bukata.

Yana daya daga cikin wadanda suka jagoranci sulhunta tsakanin dan takarar shugaban kasa a tutar jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Muryar malamin tana isa wurare da yawa musamman ta kafofin sada zumunta, inda maganarsa ke janyo tattaunawa da mabanbantan ra'ayi musamman ta fuskar siyasa.

Ana kallonsa a matsayin wani mutum mai jawo ce-ce-ku-ce

Sheikh Abdullahi Bala Lau

Asalin hoton, Bala Lau Facebook

Shi ne shugaban kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa Iqamatus Sunnah na Najeriya.

Kungiyar da yake jagoranta tana da mabiya masu dumbin yawa a fadin kasar da ma makotanta. Sheikh Bala Lau yana daya daga cikin malaman da ake ganinsu a ofisoshin gwamnati.

Sunansa ya bayyana a cikin jerin sunayen da jaridar Premium Times ta bayyana cewa sun karbi kudin makaman da ake zargin Sambo Dasuki ya raba a dab da zaben 2015.

Bishop Matthew Hassan Kukah

Asalin hoton, Hassan Kukah Facebook

Babban malamin addinin Kiristanci ne da aka haifa a shekarar 1952 a karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna.

Marubuci ne kuma jagora ne a cocin Roman Katolika da yake da gun ibada a jihar Sokoto.

An sanya shi a cikin kwamitin gyararrakin zabe na 2009 bayan ya zama sakataren taron masana da aka yi don gyara harkokin siyasa daga shekarar 2005.

Matthew Kukah na daya daga cikin wadanda suka jagoranci sulhun da ya gudana tsakanin Alhaji Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo.

Pastor Ayodele Joseph Oritsejafor

Asalin hoton, Pastor Ayodele Joseph Oritsejafor

Bayanan hoto,

Ana yawan ganin Pastor Ayodele Joseph Oritsejafor a matsayin mai shiga lamurran gwamnati lokacin Goodluck Jonathan

Shi ne wanda ya assasa majami'ar "World of Life Bible Church" kuma shi ne babban pastor a cikinta. A shekara ta 2010 ya zama shugaban kungiyar Kiristocin Najeria da ake kira da CAN.

Ya taka rawa muhimmiya a zaben da ya gudana na 2015 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasara. Muryarsa na da karfi sosai a tsakanin kiristocin Najeriya, ba iya Arewa kawai ba.

Apostles Suleman Johnson

Asalin hoton, Apostle Sulaiman Facebook

Shi ne jagoran "Omega Fires Ministries". Malamin na addinin Kirista ya yi maganganu a kan zaben 2019 inda ya ce 'yan Najeriya suna bukatar su yi addu'o'i idan har suna bukatar zaben ya gudana cikin sauki.

Yawan bayaninsa akan abin da yake ganin za su faru ya sanya yake da murya a fadin kasar nan tare da cewa cocin da ya assasa a shekarar 2004 tana garin Auchi da ke jihar Edo.

Akwai malamai da yawa da ake ganin muryoyinsu sun fi tasiri a jihohinsu amma ba kasa ba.

Sannan akwai malaman da tare da mabiyansu da yawa ba sa shiga harkokin siyasa saboda suna ganin su iyayen al'umma ne musamman a bangaren Arewa.