Kisan Khashoggi: Yariman Saudiyya ba shi da hankali, in ji sanatocin Amurka

Mohammed bin Salman Hakkin mallakar hoto Reuters

Sanatocin Amurka sun ce yanzu sun hakikance cewa yariman Saudiyya na da hannu cikin kisar Jamal Khashoggi bayan da hukumar leken asirin kasar ta gabatar masu da wani bayani.

A wata caccaka da ya yi, sanata Lindsey Graham ya ce ya tabbatar Mohammed bin Salman na da hannu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi.

Sanatan na jam'iyyar Republican daga yankin South Carolina ya bayyana yariman na Saudiyya a matsayin mutum 'mai ta'adi', 'mahaukaci', kuma 'mai hadari'.

Saudiyya dai ta gurfanar da mutum 11 gaban kotu, amma ta musanta cewa yariman na Saudiyya na da hannu cikin al'amarin.

Me sanatocin suka ce?

Daya daga cikin sanatocin na Amurka ya ce ba zai kara goyon bayan kasar Saudiyya a yakin da take yi a Yemen ba, ko kuma sayar wa kasar da makamai, matukar yariman na kan mukaminsa.

Wani sanatan kuma mai suna Bob Corker ya shaida wa 'yan jarida cewa a yanzu ba ya tantama ko kadan, cewa Mohammed bin Salman ne ya bayar da umurnin aiwatar da kisan.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wakilin BBC Frank Gardner ya yi sharhi kan abinda ka iya faruwa ga MBS

Mista Corker ya ce shugaban Amurka Donald Trump ya nuna goyon baya ke nan ga kisan dan jaridan saboda ya ki sukar yariman na Saudiyya.

Majalisar dai tana shirin kada kuri'a kan wata shawara ta daina tallafa wa kawancen dakaru karkashin Saudiyya wadanda ke fada da 'yan tawaye a Yemen.

Mene ne hukumar CIA ta ce?

Hukumar leken asiri ta CIA ta ce alamu sun nuna cewa yarima Mohammed bin Salman ne ya bayar da umurnin kashe Khashoggi.

Hukumar tana da shaidu da ke nuna cewa yariman ya yi musayar sakonnin tsakanin sa da Saud al-Qahtani, mutumin da ake zargin sa da jagorantar kisan.

sai dai a a wani zama da majalisar ta yi a makon jiya, sakataren waje na Amurka Mike Pompeo da sakataren tsaron kasar James Mattis sun shaida wa sanatoci cewa babu wata tabbatacciyar hujja kai-tsaye da za ta nuna cewa akwai hannun yariman a kisan Khashoggi.

Shugaba Trump ya ce bayanan hukumar CIA din kan yariman Saudiyya ba cikakku ba ne.

A ranar 20 ga watan Nuwamba Trump ya ce "Zai iya yiwuwa yariman yana da masaniya game da wannan mummunar al'amari - Kila ya sani, kila kuma bai sani ba."

Wane ne Jamal Khashoggi?

A matsayin sa na shahararren dan jarida, ya yi aikin kan muhimman labarai da dama, har da na mamayar da tarayyar Soviet ta yi wa Afghanistan da kuma na rayuwar Osama bin Laden, ga kafafen yada labaru da ke Saudiyya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jamal Khashoggi ya je Istanbul ne domin samun takardun aure

A tsawon shekaru masu yawa, dan jaridan wanda ya zauna a Amurka, na da alaka ta kut da kut da gidan sarautar Saudiyya, kuma ya kasance mai bai wa gwamnati shawara.

Sai dai ya samu rashin jituwa da gidan sarautar, inda ya tsere zuwa Amurka da zama a bara. a Amurka din ne ya rinka rubuta sharhi a kowane wata a jaridar Washington Post, wanda a cikin sa ya rinka sukar manufofin yarima Mohammed bin Salman, daga ciki har da yakin da kasar ke yi a Yemen.

Labarai masu alaka