Matar da aka hana ganin gawar danta
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Asibitoci na tsare majinyata kan rashin kudi a Najeriya

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An hana Ogosi da Chinonso Osegbo ganin gawar dansu saboda ba su biya kudin asibiti ba.

Chiamaka Ogbodo ta kwashe sama da shekara guda a asibiti bayan da ta haifi danta kuma ta gaza biyan kudin jinya.

Ana tunanin ana rike dubban majinyata a fadin Najeriya saboda matsalar kudi.

A fadin duniya, dubban marasa lafiya ne irin wannan matsalar ke shafa duk shekara musamman ma a yankin Afirka kudu da Sahara da kuma nahiyar Asiya.

Labarai masu alaka