Ma'aikaciyar BBC ta kashe kanta

Vicki Archer Hakkin mallakar hoto Vicki Archer

An tsinci gawar wata ma'aikaciyar rediyo a BBC wadda ta dakatar da shirinta a lokacin da ake yada shi.

Vicki Archer, 41, 'yar kimanin shekara 41, na da matsalar damuwa kuma sau biyu tana yunkurin kashe kanta, in ji wani bincike da wata kotu ta yi.

A watan Augustan da ya wuce, an gan ta a rataye a gidanta, bayan ta tura wa abokin aikinta sako cewa ita fa ranta a bace yake.

An ce mijin mahaifiyar matar, wadda ke da 'ya'ya uku, ne ya gano gawarta a gida bayan ta bar wajen aikinta.

Hakkin mallakar hoto Geoff Ward
Image caption Iyalanta sun ce Vicki Archer macece mai kirki kuma uwa ta gari

Bayan da mijin mahaifiyarta ta ya gan ta ya yi kokarin ya ga ya ceto ta amma hakan bai yiwu ba saboda ta riga ta mutu.

Daga nan ne kuma mahaifiyarta ta zo wajen inda ta ce tun da safe ta tafi aiki.

Hakkin mallakar hoto Vicki Archer
Image caption Vicki Archer ta shafe shekara 20 tana aiki

Mr Ellery ta ce "mun samu labarin cewa Victoria ta yi yunkurin kashe kan ta har sau biyu a baya, kuma tana fama da lalurar damuwa."

A cewar ta, "bai zama dole mu ce sai mun yi bincike mun gano me ke damun ta a rayuwa ba."

Victoria dai ta bar wajen shirin da take gabatarwa, inda aka zaci ko ta dan zaga ne, amma kuma sai aka ji shiru.

Wannan dai wani babban tashin hankalin ne ga iyalanta musamman ma 'ya'yanta.

Iyalanta sun ce har yanzu sun kasa yarda cewa Vicki ta mutu.

Uwa ta gari ce, kazalika 'ya mai biyayya, sannan ita ta kowa ce saboda faran-faran din ta, in ji su.

Hakkin mallakar hoto Geoff Ward

Labarai masu alaka