Ana sace 'kashi 60' na hasken wutar lantarkin Liberia

People drive through the dark in the West Point slum, where few homes have electricity, on August 15, 2014 in Monrovia, Liberia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akasarin mazauna Monrovia ba su da hasken wutar lantarki

Hukumar samar da hasken lantarkin Liberia ta yi zargin cewa jama'a na sace kimanin kashi 60 na hasken wutar lantarkin kasar a duk shekara ta hanyar jan sa daga layukansa zuwa gidaje da ofisoshinsu ba bisa ka'ida ba.

Hakan ya sa kasar na yin asarar kusan $35m aduk shekara, a cewar jami'an Liberia Electricity Corporation.

Sun kara da cewa satar wutar lantarkin ta hana hukumar samar da hasken lantarkin samun kudaden da za ta ci gaba da amfani da su wurin rarraba hasken lantarki zuwa wasu yankuna.

Liberia nakokarin sake gina tasoshin samar da hasken lantarkinta, wadanda aka rusa lokacin yakin basarar da aka yi tsakanin shekarar 1989 zuwa 2003.

Amurka na bai wa kasar tallafin kudi da kayan aiki domin kara rarraba hasken lantarki zuwa sassan da ba su da shi, a shirin nan na samar da hasken lantarki da tsohon Shugaba Barack Obama ya kaddamar na samar da lantarki ga mutum miliyan 50 da ke yankin Afirka da ke kudu da hamadar sahara zuwa shekarar 2020.

Sai dai har yanzu kashi 12 cikin 100 na 'yan Liberia ne - da kuma kasa da kashi 20 na mazauna babban birnin kasar, Monrovia - ne suke da lantarki, daya daga cikin mafi kankanta a duniya.

Gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin samar da lantarki ga kashi 70 cikin 100 na mazauna birnin Monrovia wanda aka kiyasta cewa mazauna cikin sa za su kai miliyan daya zuwa shekarar 2030.

Labarai masu alaka