Facebook ya shiga yarjejeniyar sirri kan bayanan mabiyansa

facebook boss Hakkin mallakar hoto Getty Images

An gano wasu sakonnin email masu nuna yadda Shugaban Facebook da mataimakinsa suka bai wa wasu masu hade-haden manhajoji bayanan masu amfani da shafukan na Facebook inda suka hana wasu, a cewar wani dan majalisa.

Kwamitin majalisar Amurka ya saki wasu takardu masu dama a intanet a kan hakan.

Sun kuma bayyana cewa Facebook da gangan ya maida sanin bayanan sirri na amfani da shafukan 'abu mai wahala' ga masu amfani da shafin ta manhajar Android.

Amma Facebook ya musanta wannan zargin.

Ya kuma bayyana cewa an gabatar da takardun ta 'hanya mai rikitarwa' kuma akwai bukatar karin bayanai.

An samu sakonnin na emails din ne daga shugaban kamfanin Six4Three wanda yake amfani da Facebook da kwamitin shafukan intanet da sadarwa da kuma kafafen yada labarai da wasanni ne ya fallasa su.

An fallasa kimanin takardu 250 wadanda wasu daga cikinsu 'sirri ne matuka'.

Labarai masu alaka