An yi hazon launin shan-shan-bale a Ingila

Scarborough bay Hakkin mallakar hoto Beverley Senturk
Image caption Yanayin kasar yasa aka samu kyawawan hotuna daga gabar teku, kamar hoton da Beverley Senturk ta dauka daga Scarborough dake arewacin Yorkshire.

Wadanda suka yi sammako a safiyar Alhamis a Ingila, sun sha kallo sosai ta yadda rana ta bullo bayan sararin samaniya ya canza zuwa launin shan-shan bale, da ruwan hoda.

Masu hasashen yanayi na BBC suka turo wadannan hotunan daga gabar tekun arewacin Yorkshire har zuwa Dorset inda suke daukar hotunan irin wannan yanayin da ba a saba gani ba.

Hakkin mallakar hoto Medievaljeremy
Image caption Mai hasashen yanayi na BBC Medieval Jeremy ya dauki wannan hoton mai cike da hazo mai launin shan-shan bale a garin Queniborough da ke Leicestershire

Mai labarun hasashen yanayi ta BBC watau Sarah Keith-Lucas ta bayyana cewa daya daga cikin abinda yasa aka samu haka shi ne sauyin yanayin da aka samu ne daga bangaren tekun Atlantika.

Ya kuma bayyana cewa "Karin iskar da ke tashi zuwa teku, zai iya ja a samu kwayoyin gishiri zuwa sararrin samaniya," hakan yake ja haske yana kara watsuwa sosai, sai ya sa a samu tsayayyun launi irin ruwan hoda da shan-shan bale a lokacin fitowar rana da faduwarta.

Hakkin mallakar hoto Octopok
Image caption Wannan hoton an dauke shi ne a Bridlington da ke gabashin Yorkshire
Hakkin mallakar hoto Kingfisher Whisperer
Image caption Kingfisher ya dauki wannan hoton a Coventry

Dalilin da yasa launin sama yake canzawa- inji Sarah Keith-Lucas, ma'aikaciyar BBC a bangaren hasashen yanayi.

Gajeren ratsin shudi da kuma launin shan-shan bale yana saurin watsuwa, amma dogon ratsin ruwan lemo da kuma ja basu sauran watsuwa, saboda haka suke ratsa idanuwanmu.

Wannan yana nufin sararin samaniya kan koma launi ja, ruwan hoda ko kuma ruwan lemu a lokacin fitowa da faduwar rana.

Ana samun takamaiman laununkan da ake samu ne a lokacin fitowar rana a bisa dalilan kura, gurbacewar muhalli, yayyafi da kuma haduwar giza-gizai, a wani lokacin za su iya zama ruwan shan-shan bale da ruwan hoda ba wai lallai sai ruwan lemu ko ja kamar yadda aka fi sani ba.

Wannan zai iya zama daya daga cikin abinda idonmu yake nuna mana, na ratsin ruwan hoda da ke haskaka sararin samaniya, haka kuma wadannan giza-gizan masu ruwan hoda suna ratsa giza-gizai masu launin shudi.

Haduwar ruwan hoda da na shudi kan saka sararin samaniya ya zama ruwan shan-shan bale.

Hakkin mallakar hoto Rachael Reynolds
Image caption Rachael Reynolds ta dauki wannan hoton a tashar jirgin kasa ta Chester
Image caption Sararin samaniya ya zama launin shan-shan bale, a safiyar Alhamis a Dorchester da ke yankin Dorset.
Hakkin mallakar hoto Avril
Image caption Mai hasashen yanayi ta BBC Watcher Avril ta wallafa wannan hoton daga Inkberrow dake Worcestershire
Hakkin mallakar hoto Thedogwalker
Image caption Me hasashen yanayi na BBC Thedogwalker ya dauki wannan hoton ratsin ruwan hoda da ruwan shan-shan bale a sararin samaniya a Southam da ke Warwickshire
Hakkin mallakar hoto James_H
Image caption Giza-gizai a kudancin Yorkshire inda aka samu ratsin ruwan hoda da na shan-shan bale
Hakkin mallakar hoto Graham's vista
Image caption Ruwan shan-shan bale a Borough: Graham Vista ne ya dauki wannan hoton a Sutton Coldfield

Labarai masu alaka