Amsar tambayoyinku a kan runfunan zabe a Najeriya

A picture taken on September 22, 2018 shows as an electoral officer raises a ballot to count results in Ede, near Osogbo, Osun State in southwest Nigeria.

Asalin hoton, Getty Images

Wannan makala ce da muka yi bayan da muka bukaci ku aiko da tambayoyinku kan abin da kuke son sani dangane da duk abun da ya shafi Rumfunan Zabe a Najeriya.

Hukumar ta INEC ce ke da hakkin shirya zabe a fadin tarayyar Najeriya.

BBC Hausa ta mika tambayoyinku ga Mallam Aliyu Bello, wanda shi ne kakakin Hukumar Zabe ta Najeriya, INEC, wanda kuma ya yi kokarin amsa wasu tambayoyi da masu saurare suka aiko.

'Wai shin za a yi amfani da na'urar Card Reader?'

Tambaya ce da muka samu daga Umar Abubakar da Sani Garba da Ishaq Abubakar Kazaure

Kwarai za ayi amfani da na'urar Card Reader a zaben 2019 da ke gaba, kuma wani abu ma da aka kara samun ci gaba shi ne hukumar zabe ta kara inganta na'urorin tantance masu zabe - wato card reader - ta yadda ba za a samu jinkiri wajen tantance yatsun masu jefa kuri'a ba.

Kuma, an inganta ta kwarai sama da yadda aka yi amfani da ita a baya, ta yadda zaben 2019 zai kara samun saukin gudanarwa, da kuma tagomashin da ya dace.

Asalin hoton, Getty Images

2 - Cunkoso a rumfar zabe- Batun karin rumfunan zabe a Najeriya?

Wannan ma tambaya ce da mutane da dama suka aiko

Akwai tanadi da hukumar zabe ta yi don ta samu saukin gudanar da zabubbuka, ba tare da an dauki tsawon lokaci ko an samu jinkiri wajen kada kuri'a ba, musamman a rumfunan da aka samu yawan su ya kai kamar 1,000 ko fiye.

Hukumar Zabe sai ta tsara cewar za a yayyanka rijistar ya zuwa mutum dari uku-uku, kuma sai a samu karin ma'aikatan da za su gudanar da wadannan zabubbuka a wuri daya.

Amma fa duka a cikin rumfa daya ake, ba wai an kirkiri sabuwar rumfa ce ta musamman ba, illa wadansu rukunnan jefa zabe ne aka yi don a taimaka wa jama'a su samu saukin jefa kuri'a, a samu kammala zabe cikin lokacin da ya dace.

Batun raba rumfuna zuwa kananan rukunnai don gudanar da zabe wannan wani tanadi ne da Hukumar Zabe ta yi, don samun nasarar gudanar da zabe cikin karamin lokaci.

Duk rumfar da ta wuce mutane 900 zuwa 1,000, sai a kara yawan ma'aikata yadda ko wane ma'aikaci zai kula da masu kada kuri'a akalla 300 ne, saboda haka, wannan tanadi ne da aka yi shi don a taimaka wajen gudanar da zabe ayi su cikin hanzari da kwanciyar hankali.

A duk dan kafar da aka sa zaben 2019 a gaba, ba a maganar karin rumfuna a halin yanzu, illa wani tanadi ne da za'a yi shi kila bayan zaben 2019.

Asalin hoton, Getty Images

Yadda a ke gudanar da zabe

Wasu masu sauraron sun aiko da tambayoyi kamar haka:

Ko ya dace idan ka zo kada kuri'a wakilin jam'iyya ya nuna inda tambarin jam'iyyar yake ko kuma ya kada ma da kansa?

Shin ko akwai adadin mutanen da aka kayyadewa kowace rumfa? Saboda a garinmu rumfa daya kawai muke da ita.

Batun wakilin jam'iyya ko party agent ya nuna wa mai jefa kuri'a irin alamar jam'iyyarsa a kan takardar takadar zabe, wannan laifi ne, saba doka ne ba abu ne da aka yadda ayi ba.

Domin haka ya kai ga matakin tamkar kana nunawa mai jefa kuri'a gurin da zai jefa kenan, kuma, zabin mai jefa kuri'a ne ya zabi jam'iyyar da yake so daga shi sai Allah ba tare da wani ya sani ba.

Doka ba ta ce ga mafi karancin yawan mutanen da za'a samu a rumfa ba, kuma ba ta nuna ga mafi nisan zangon jama'an da za'a samu a rumfa ba, illa jama'a ke da damar wata rumfa ta fi maka kusa domin yin rijista da jefa kuri'a ranar zabe.

Saboda haka mutane su kan karkasu ne gwargwadon yawan yadda suka zama a doron kasa; kamar ina yafi maka kusa, don me kayi rijista a wannan wuri, wannan zabi ne na me jefa kuri'a.

Sai dai tanadin Hukumar zabe shi ne a duk lokacin da ta ga rumfar ta yi girman da ya kai a dan yayyanka ta yadda ranar zabe za a samu gudanar da zabubbuka a cikin sauki, za ta yi haka,

Za ta kuma tura karin ma'aikata domin a samu damar gudanar da zabe a wannan rumfa, ba tare da an samu wani tawaya ko jinkiri ba.

Asalin hoton, Getty Images

Tanadin da dokar zabe ta yi - Ga wasu jerin tambayoyin ma daga wajen masu ibiyarmu da ba su sanya sunayensu ba

- Wadanne irin dokoki da ka'idoji ne da mu masu kada kuri'a bamu san da suba? A sanar damu domin gujewa husuma cikin rashin sani.

- Wane nau'in jami'an tsaro za a kawo? Sojoji ko 'yan sanda ko civil defence? Karfe nawa jami'an zaben zasu zo, sannan muna bukatar lambar korafi ta INEC.

- Shin wace hanya hukumar zabe ta ajiye game da aringizon kuri'a a rumfunan zabe da zarar wani mutum ya gani ta ya zai sanar da hukumar zabe.

Tsarin da za a yi amfani da shi a zaben 2019 ya bambanta da tsarin da aka yi amfani dashi a zaben 2015.

A wannan karon, duk mai jefa kuri'a da zarar ya zo an tantance shi da na'urar card reader, sai a ba shi kuri'arsa kai tsaye, wato ballot paper, ya shiga ya kada wa jam'iyyar da yake so ba tare da ya yi jinkiri ba.

Idan mutane ba su manta ba a zaben 2015 in an tantance ba mai niyyar yin zabe kuri'a sai ya sa ka saurara na wani tsawon lokaci, kana ka sake dawowa ka hau layi a bayar da kuri'ar ya shiga ya jefa.

Amma a wannan karon, an sauya kawo abin yadda za a bayar da kuri'ar mutum ya jefa ba tare da wani jinkiri ko bata lokaci ba.

Idan ba a manta ba, za a fara zaben shugaban kasa ne a ranar 16 ga Fabarairun 2019, yayin da kuma za a yi zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi, a ranar 2 ga watan Maris na 2019.

Idan mutum ya yi rijista a rumfa, a wannan rumfar zai je ya jefa kuri'a, babu damar a yi rijista a nan, washegari a tafi wata rumfa a jefa kuri'a kenan.

Domin a gun da mutum ya yi rijista ne sunansa zai fito, muddin ba sunan mutum a cikin jerin masu jefa kuri'ar rumfar da ya yi rajista, to ba zai sami damar yin zaben a wani wuri na daban ba.

Asalin hoton, Getty Images

Karin bayani kan yadda za a gudanar da zaben 2019

- Tambayata a nan ita ce, wai Najeriya ba ta iya samar da hanyar saukakawa talakawa wajen samar da na'ura domin gudanar da zabe?

- Yaushe zaa fara shirin daukar malaman aikin zabe? Masu wannan tambayar ba su fadi sunayensu ba

Yana da kyau masu jefa kuri'a su gane irin ka'idojin da hukumar zabe ke aiki da su wajen fayyace wa musamman a zaben shugaban kasa da na gwamnoni.

Ka'idojin guda biyu ne: Ka'ida ta farko ita ce dan takarar ya samu mafi rinjayen kuri'un da aka kada, wanda duk ya samu fifikon kuri'u a zaben da aka yi kaga ya cika rukunin farko.

Yana kan hanyarsa ta zama mai nasara a wannan zabe kenan.

Ka'ida ta biyu ita ce ya samu akalla daya bisa hudun adadin kuri'un da aka jefa, a cikin adadin biyu bisa uku na rukunnan mazabun da ke karkashinsa.

Misali a zaben gwamna, a ce kuma jihar na da kananan hukumomi 12, wajibi dan takarar da zai zama gwamna ya sami akalla daya bisa hudun kuri'un da aka jefa a kananan hukumomi takwas kenan.

Da wannan ne hukumar zabe take aiki ta fayyace wa ya lashe zaben.

Shi yasa a wani lokaci ka ke ganin ana daukan lokaci kafin Hukumar Zabe ta bayyana waye ya ci, domin wajibin ta ne ta yi dukkan kididdiga da kidayar da ta dace domin ta tantance, ta kuma tabbatar an bi wannan doka, kafin ta fayyace cewa ga wanda Allah Ya ba nasara.