Zaben 2019: Kun san iyalan Shugaba Muhammadu Buhari?

Muhammadu Buhari da 'ya'yansa mata Halima da Zahra da Hanan da jikarsa Zulaiha da dansa Yusuf da surukansa Ahmed Indimi da Aminu Sheriff Hakkin mallakar hoto INSTAGRAM/ZAHRA BUHARI
Image caption Muhammadu Buhari da 'ya'yansa mata Halima da Zahra da Hanan da Noor da jikarsa Zulaiha da dansa Yusuf da surukansa Ahmed Indimi da Aminu Sheriff

Shugaba Muhammadu Buhari ya auri matarsa ta farko Safinatu a watan Disambar shekarar 1971.

An haifi Hajiya Safinatu ran 11 ga watan Disambar shekarar 1952 a garin Jos na jihar Filato amma 'yar asalin garin Mani ce ta jihar katsina.

Sunan mahaifinta Alhaji Yusufu Mani, mahaifiyarta kuwa sunanta Hajiya Hadizatu Mani.

Ta yi karatu a Makarantar Horon Malamai (WTC) a Katsina inda ta kai mataki na biyu a shekarar 1971.

Safinatu ta fara haduwa ne da Muhammadu Buhari lokacin tana da shekara 14.

A lokacin Shugaba Buhari Manjo ne a rundunar sojin Najeriya, sai ya raka abokinsa marigayi Manjo Janar Shehu Musa 'Yar'aduwa gurin mahaifin Safinatu.

A lokacin baban Safinatu, Alhaji Yusufu Mani yana aiki a Legas a matsayin sakataren Alhaji Musa 'Yar'aduwa wanda shi ne Ministan harkokin Legas na wannan lokacin a jamhuriya ta farko.

Tun daga wannan ziyarar soyayya ta kullu a tsakanin Muhammadu Buhari da Safinatu Yusufu.

Hakkin mallakar hoto Buhari Family
Image caption Muhammadu Buhari da matarsa ta fari Safinatu da 'ya'aynsu Zulaihatu da Nana Hadiza da Fatima da Safina da kanin matarsa Nasiru

Yakin basasar Najeriya ya barke ne dan lokaci kadan bayan haduwar Muhammadu Buhari da Safinatu Yusuf, kuma yana daya daga cikin sojojin da aka tura don fafatawa a fagen yakin a bangaren Najeriya.

Don haka, sai da aka gama yakin a shekarar 1970 aka daura aurensu a watan Disambar 1971.


'Ya'yansu da jikokinsu

Sun haifi 'yarsu ta fari Zulaiha wacce aka rika kira Magajiya.

Zulaiha ta rasu a shekarar 2012 kuma ta haifi 'ya'ya hudu- Halima (Amira) da Junaid da Muhammadu Buhari da Zulaiha.

Zulaiha ta sha fama da cutar amosanin jini kuma ta rasu ne sakanamon haihuwa.

Gidan talbijin na AIT ya taba wani rahoto a watan Janairun 2015 daf da babban zaben kasar, inda aka dinga batun Zulaiha da cutarta ta sikila.

Al'amarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, mutane da dama na ganin duk zafin siyasa bai kamata a hada lamarin da marigayiyar 'yar Shugaba Buharin ba.

Hakkin mallakar hoto NANA BUHARI
Image caption Fatima Muhammadu Buhari

Sai 'yarsu ta biyu Fatima wacce take da yara shidda- Nana Aisha da Khadija da Hauwa da Maryam da Safina da Muhammadu Gidado.

Sai dansu na uku kuma shi ne namiji tilo Musa, wanda ya rasu tun yana jariri.

Hakkin mallakar hoto NANA BUHARI
Image caption Nana Hadiza Muhammadu Buhari

Daga shi sai Nana Hadiza wacce take da yara hudu- Amina Amal, da Halima da Mahmoud da Zulaikha.

Hakkin mallakar hoto NANA BUHARI
Image caption Hajiya Rakiya Adam, yayar Shugaba Muhammadu Buhari da Nana Hadiza Muhammadu Buhari da jaririyarta

Sannan sai Safina (Lami) wacce ta ke da yara biyu - Isa (Khalifa) da Isma'ila (Fahd).

Hakkin mallakar hoto NANA BUHARI
Image caption Safina (Lami) Muhammadu Buhari da Maigidanta Abubakar Sama'ila Isa

Hajiya Safina matar Muhammadu Buhari ta farko ta rasu a shekarar 2005 tana da shekara 53 a duniya, sai dai a lokacin da ta rasu ba ta tare da Shugaba Buhari.


Aurensa da Aisha Buhari

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar BBC da Aisha Buhari ta tayar da kura

An haifi Aisha Halilu ran 17 ga watan Fabrairun 1971 a jihar Adamawa da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kakanta Alhaji Muhammadu Ribadu shi ne ministan tsaron Najeriya na farko.

Ta yi digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a fannin Public Admimistration, sai ta yi digirinta na biyu a kan harkokin kasashen waje.

Ta yi difloma a fannin kwalliya a makarantar koyon ado ta Carlton Institute da ke Windsor a Birtaniya, da kuma wata makarantar koyon gyaran jiki ta Academy Esthetique da ke Faransa.

Hakkin mallakar hoto NANA BUHARI
Image caption Aisha Muhammadu Buhari da wasu daga cikin 'ya'yan Shugaba Muhammadu Buhari

Kafin maigidanta ya zama Shugaban Najeriya, tana da shagon gyaran jiki da kwalliya mai suna Hanzy Spa a jihar Kaduna.

Ta wallafa wani littafi na koyar da kwalliya da gyaran jiki wanda Hukumar da ke kula ta makarantun kimiyya da fasaha ta Najeriya ta sa shi a cikin manhajar da makarantun za su yi amfani da shi.

Aisha ta haifi 'ya'ya biyar da Muhammadu Buhari.

'Mace mai jawo ce-ce-ku-ce'

Ana yi wa Hajiya Aisha Buhari kallon mace mai yawan jawo ce-ce-ku-ce kan al'amuran da suka shafi mulkin maigidanta.

Ta taba wata hira da BBC Hausa inda ta ce wasu 'yan tsirarun mutane sun mamaye gwamnatin mijninta, Shugaba Muhammadu Buhari, suna hana ruwa gudu.

Akwai kuma lokacin da ta soki jam'iyya mai mulki ta APC dangane da yadda ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta a 2018.

Hakkin mallakar hoto INSTAGRAM/MAMZABEAUTY
Image caption Halima Muhammadu Buhari

Ta haifi 'yarta ta fari Halima wacce take da diya mace Aisha (Ayush).

Hakkin mallakar hoto INSTAGRAM
Image caption Yusuf Muhammadu Buhari

Sai Yusuf mai bi wa Halima, wanda ya kammala karatunsa a Birtaniya.

A watan Disambar 2017 ne Yusuf ya hadu da tsautsayi inda ya yi mummunan hatsari da babur din tsere a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Yusuf dai ya shafe tsawon lokaci yana jinya, amma daga bisani ya samu lafiya sosai.

Hakkin mallakar hoto INSTAGRAM/ZAHRA_BUHAR_INDIMI
Image caption Zahra Muhammadu Buhari

Sai Zarah Buhari matar wacce take auren Ahmad Indimi dan fitaccen attajirin nan na Najeriya, kuma ta haifi da guda daya Muhammad (Ra'is).

A iya cewa Zahra ce ta fi yin fice a cikin 'ya'yan shugaban, saboda yadda aka san ta sosai sakamakon yawan amfani da shafukan sada zumunta kamar Twitter da Instagram da Facebook.

Hakkin mallakar hoto INSTAGRAM
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari da 'yarsa Amina da jikarsa Zulaiha

Aisha wacce ake nkira da Hanaan ce ke bin Zahra, sannan sai 'yar autar shugaban wato Amina (Noor).

Hanaan da Noor ba su yi aure ba tukunna.

Hakkin mallakar hoto NANA BUHARI
Image caption Amina (Noor) Muhammadu Buhari da Nana Hadiza Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na da 'ya'ya 10 - takwas mata, biyu maza.

Kuma guda biyu a cikin 'ya'yan nasa sun rasu-- Da Zulaiha da Musa.

Shugaban kuma yana da jikoki 18.

Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI
Image caption Aisha ita ce matar Muhammadu Buhari ta biyu

Karin Labaran da za ku so ku karanta:


Bayanai da hotuna: Daga iyalan shugaban da kuma wasu majiyoyi masu karfi.