OPEC za ta rage fitar da mai

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar ta OPEC ta rage yawan man da take fitarwa ne domin daga farashinsa

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, da kuma wata kungiyar kasashe da ke kawance da kungiyar da ta hada da Rasha, sun amince a rage yawan man da ake samarwa zuwa ganga miliyan daya da dubu dari biyu a rana, ko kuma kashi daya cikin dari na man da ake samarwa a duniya

Farashin danyen mai ya karu zuwa fiye da kashi hudu cikin dari yayinda labarin ya bayyana daga wani taron ministocin makamashi a hedikwatar Kungiyar OPEC a Vienna

Mambobin kungiyar sun dauki wannan matakin ne bayan faduwar farashin man da aka samu na kashi talatin cikin dari a makonni shidan da suka gabata da kuma hasashen da ake yi na tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin duniya zai yi a badi

Kasashe da dama kamar irinsu Najeriya sun dogara da man ne domin samun kudaden shiga.