'Yan sanda da masu zanga-zanga na artabu a France

'Yan Faransa na cewa rayuwa ta yi tsada amma kuma albashi yana nan a tsumbure
Image caption Masu zanga-zangar na rera wake na nuna kin jinin gwamnatin shugaba Macron

Daruruwan masu sanye da rawayar singileti sun taru a tsakiyar birnin Paris na kasar Faransa domin ci gaba da zanga-zangar nuna kyamar gwamnati.

Wannan dai shi ne karo na hudu da masu zanga-zangar ke haduwa a karshen mako domin yin tur da kudirin gwamnatin na kara harajin man fetur da tsadar rayuwa.

Sai dai kuma yawan masu zanga-zangar ya ragu sosai idan aka kwatanta da makon da ya gabata.

Har wa yau, yawan masu zanga-zangar a sauran biranen kasar ma ya ragu.

Yanzu haka ana artabu tsakanin masu zanga-zangar kimanin dubu biyu da 'yan sanda a dandalin Champs-Elysées, inda 'yan sandan ke kokarin hana su zuwa gidan shugaban kasa.

An kama daruruwan mutane tun ma kafin zanga-zangar ta yau.

Da ma dai ministan cikin gida na Faransar, Christophe Castaner ya yi gargadin cewa ba za su laminta da duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye ba.

A farkon makon da ya gabata ne shugaba Emmanuel Macron ya sanar da janye aniyar gwamnatinsa na kara yawan harajin man fetur din da ya janyo rikicin da aka dade ba a gani ba a kasar.