'Yan awaren Kamaru sun fitar da 'takardun kudi na intanet

Hakkin mallakar hoto Ambacoin / Facebook

'Yan awaren yanki mai amfani da turancin Ingilishi na Kamaru sun kaddamar da 'takardun kudi na intanet mai suna AmbaCoin, kamar yadda wani rahoto na jaridar intanet ta Quartz ya bayyana.

'Yan awaren na fafutukar kafa wata kasa mai suna Ambazoniya ne daga kasar Kamaru, kuma wannan takardar kudin na cikin matakai na baya-bayan nan a kan hanyarsu ta kafa kasar.

Ban da wannan ma, sun kaddamar da wata tuta mai launin shudi da fari har ma da takensu.

Darajar kwabo daya na AmbaCoin daidai yake da senti 25 na dalar Amurka inji jaridar ta Quartz wadda ta ce tuni aka fara odar kudin kafin a fara sayar da shi a "ranar 24 ga watan Disamba".

Kamaru na amfani ne da kudin CFA na kasashen yankin tsakiyar Afirka, wanda kuma ke da alaka ta kut-da-kut da baitulmalin kasar Faransa.

Akwai wadanda ke ganin ya kamata a daina amfani da kudin na CFA domin sun ce "kudin 'yan mulkin mallaka ne".

Labarai masu alaka