An zabi Seidou Mbombo Njoya sabon shugaban Fecafoot ta Kamaru

The headquarters of the Federation Camerounaise de Football (Fecafoot), or Cameroonian Football Federation, in Yaounde Hakkin mallakar hoto AFP

An zabi Seidou Mbombo Njoya a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Kamaru, Fecafoot a ranar 13 ga watan Disamba bayan an shafe watanni 15 babu zababben shugaba.

Sabon shugaban ya yi alkawarin tabbatar da baza komai a faifai domin ci gaban hukumar da wasan kwallon kafa a kasar.

Seidou ya lashe zaben da kuri'u 46 a cikin kuri'u 66 da aka kada, inda mai bi masa Antoine Bell ya sami kuri'u 17, sai na Nyamasi wanda ya zo na uku da kuri'u uku.

Tun bayan da aka daure tsohon shugaban hukumar Iya Mohammed a 2013, harkar kwallon kafa a Kamaru ke cikin rudani.

Image caption Seidou Mbombo Njoya

"Bayan shekaru biyar ana cikin rudani, komai ya zo karshe. Ya kamata mu dage wajen sake raya wasan kwallon kafa ta hanyar samar da wasu tsare-tsaren da zasu dawo da martabar wasan a Kamaru", inji sabon shugaban.

Sauran 'yan takarar ba su sami kuri'u ba a zaben da ya gudana a cibiyar CAF da ke birnin Yaounde.

Za a rantsar da Seidou tare da sabbin jami'an hukumar ta Fecafoot da aka zaba a cikin kwanaki masu zuwa.

Labarai masu alaka