Shugaban Eritriya ya kai ziyara Somaliya

Isaias Afwerki Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Isaias Afwerki

Shugaban kasar Eritriya Isaias Afwerki ya kai ziyara Somaliya bayan shekaru da dama da ya kai irin wannan ziyarar a baya.

Shugaban ya tattauna da takwaransa na Somaliya Mohammed Abdullahi a birnin Mogadishu babban birnin kasar.

Fiye da shekaru da dama, Eritrea ta ki amincewa da Somaliya, saboda zargin cewa Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakagida a kasar a shekarun baya, da kuma kawancen da ta kulla da Habasha da sauran kasashen yammacin duniya.

Amma sakamakon sasantawar da aka samu tsakanin Eritriya da Habasha, an samu ci gaba sosai a yankin. Jama'a da dama suna yaba wa sabon shugaban Habasha Abiy Ahmed, saboda irin rawar da ya taka wajen ganin an samu wannan sasantawar.

Shugaba Abiy ya taimaka wajen kawo karshen 'yar tsama da ke tsakanin kasashen biyu, inda kuma ya ba da shawarar su rika tattaunawa akai-akai.

A watan Yuli, Shugaba Mohammad ya ziyarci Asmara, inda shugabannin kasahen suka sa hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Somaliya, Habasha da kuma Eritrea.

Ministan watsa labarai na Eritriya ya bayyana cewa, ziyarar tarihi ta shugaba Isaias na daya daga cikin taron tuntuba wanda ya hada shuwagabannin kasashen Eritriya da Habasha da kuma Somaliya.

Ministan ya kuma wallafa hotuna a shafinsa na Titita domin nuna kasaitacciyar tarbar da aka yi wa shugaban na Eritriya.

Fadar shugaban kasar Somaliya ita ma ta bayyana a Tiwita cewa wannan ziyarar ta bude wani sabon babi ga dangantakar kasashen biyu.

A baya an zargi Eritriyar da goyon bayan 'yan tayar da kayar baya ta Al-Shabab, zargin da kasar ta dade tana musantawa.

A shekara ta 2009 ne Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa kasar takunkumi, amma a watan Nuwamba aka cire shi saboda rashin samun kwararan hujjoji da zasu tabbatar da zargin.

Ana sa ran Mista Isaias zai kai ziyara zuwa Kenya domin tattaunawa da shugaban kasar Uhuru Kenyata.

Labarai masu alaka