Boko Haram ta kai hari kauyen Maiborti

Rikicin Boko Haram ya raba miliyoyin mutane da muhallansu a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Boko Haram ta kai hari kauyen Maiborti da ke wajen Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Mayakan na Boko Haram sun kuma kona gidaje tare da tursasawa mazauna kauyen tserewa daga muhallansu.

Ba bu dai tabbacin a kan ko an rasa rai ko rauni a yayin harin da aka kai a kauyen.

Rundunar sojin kasar dai ta ce, ta mayar da martani a harin inda sojojinta na kasa da na sama suka fatattaki mayakan na Boko Haram daga kauyen.

Wannan dai shi ne hari na baya-bayan nan da kungiyar ta Boko Haram ta kai a jihar ta Borno.

Rashin tsaro dai shi ne babban batun da ke kan gaba a taron yankunan kasashen da ke makwabtaka da Najeriya da aka gudanar a Abuja, babban birnin kasar.

Labarai masu alaka