Baiwa hudu da mutane kalilan a duniya ke da su

Jerin Kwayoyin Halitta

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Wasu mutane suna da kwayoyin hallittar da suka gada daga iyayensu da suke basu damar yin wasu abubuwan da ba kowane dan adam zai iya ba

Ana samun irin wadannan mutanen masu baiwa irin ta aljanu ne kawai a litattafan tatsuniya da hikayoyi na kimiyya.

Amma mutane kadan suna da wata baiwa ta musamman inda sauran jama'a sai dai su yi mafarkin samunta.

A wani lokacin, ana kwatanta irin wannan baiwar ne da yanayin kwayoyin halitta, wani lokacin kuma da yadda jikin mutum yake sabawa da yanayin da ya tsinci kansa a rayuwa.

Ga wasu misalai 4 na irin baiwar da wasu mutane kadan suke dauke da ita a duniya.

1. Ido bude a ruwa

Da yawan mutane ba su gani yadda ya kamata idan suka bude ido a lokacin da suke iyo cikin ruwa.

Amma yara 'yan kabilar Moken wadanda suke cikin kabilu uku na gefen tekun Andaman da ke Myanmar da Thailand sun fita daban.

Mazauna wannan tsibirin an san su ne da tafiya ci-rani cikin teku saboda suna shafe fiye da shekara suna tafiya cikin jirgin ruwa, suna farautar dabbobin teku.

Wannan zai iya bayani akan dalilin da ya sa idanunsu suka saba da iyo a ruwa kuma ido a bude.

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Mafi yawancin mutane suna ganin dishi-dishi idan suka bude idanuwan su cikin ruwa

A lokacin da haske ya hadu da iska, ana karkatar da shi a lokacin da yake ratsa kwayar ido wanda iskan da ke cikin ido ta fi ta waje nauyi, amma da yake nauyin ruwa daya yake da na kwayar ido, hakan ba za ya bari ido ya gani wasai ba cikin ruwa.

Tabarau da ake amfani da shi wajen yin iyo a ruwa yana taimakawa wajen gani wasai a yayin da ake iyo a ruwa.

Wani bincike da aka wallafa a 2003 ya bayyana cewa yara 'yan kabilar Moken suna da baiwar gani cikin ruwa wasai tamkar kifin "Dolphin."

Amma wani bincike ya nuna cewa ba kamar yara ba, manya 'yan kabilar Moken wadanda a ko da yaushe suna tsaye cikin teku dauke da mashi suna kama kifi suna rasa wannan baiwar ta gani wasai a cikin ruwa.

2. Juriya ga yanayi mai tsananin sanyi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mafi yawancin mutane ba za su iya rayuwa a gidan kankara na tsawon lokaci ba

'Yan kabilar Inuit wadanda suke zama a yankin Arctic ko kuma 'yan kabilar Nenet da suke a arewacin Rasha sun saba da yanayin kankara.

Yanayin jikinsu daban yake da na sauran mutane a lokacin sanyi.

Wadannan halayyar duk daga kwayar halitta take: Idan kai ba dan kabilar Inuit ko Nenet ba ne, ko da ka je yankinsu ka shekara fiye da goma ba lallai ba ne ka zama kana da juriya ga sanyi kamar yadda asalin mazauna wannan yankin za su jure ba.

3. Rayuwa ba tare da isasshen bacci ba

Mutane da dama suna bukatar tsakanin sa'oi 7 zuwa 9 su yi bacci domin samun hutu.

Amma wani bincike da wata makaranta a Amurka ta yi a 2014 ya nuna cewa rikidar kwayoyin halitta yake sa masu wannan lamarin su yi hidimomin yau da kullum, amma bai wuce su yi baccin kasa da sa'oi 6 a dare ba.

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Masana kimiyya suna bada shawara a yi baccin sa'oi 7 zuwa 9- sai dai idan kana da matsalar rikidar halitta

4. Rayuwa a yankuna masu tsauni

Akwai wata rashin lafiya da wasu sukan samu a duk lokacin da suka hau wuri mai tsayi kamar tsauni ko jirgin sama.

Rashin lafiyar ta kan fara ne da ganin jiri sai kuma zazzabi.

Mazauna garin Andean wadanda suke zama a tsauni mai tsawon mita 5000 suna kiran wannan rashin lafiya da sunan "Soroche"- duk wanda ya je tsauni mai tsawo ya san abin da ake nufi da wannan.

Wannan rashin lafiya dai tana faruwa ne sakamakon rashin isasshen iska, wanda iska yana ragewa idan a duk lokacin da mutum yake hawa sama.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane suna hawa bisa tsauni dauke da akwati

Alamar wannan rashin lafiyar ta hada da ganin jiri, ciwon kai, rashin numfashi da kyau, da kuma saukar jini.

Amma binciken da aka gudanar akan kabilar Quechua da ke tsaunin Andes da kuma kabilar Tibetan da ke tsaunin Himalayas ya nuna yadda yanayin zamansu a inda Allah ya hallicce su yake sa suna rayuwa a tsaunuka ba tare da wata matsala ba.