Shugaban kasa ya amince mata su zubar da ciki a Ireland

Woman at clinic

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban Ireland Michael D Higgins ya sanya hannu kan kudurin dokar da ya halasta zubar da ciki a kasar dukkan matakai a majalisar dokokin kasar.

Kudurin dokar zai ba da dama a zubar da cikin da bai wuce mako 12 ba, idan aka lura dan tayin yana da larura ko kuma mahaifiyarsa na fuskantar barazanar rasa ranta.

Za a abi wa likitoci biyu damar duba mai cikin tun ba shi da kwari sannan an cire bangare da ya tanaji hukunci kan duk wanda ya zubar da cikin daga kudurin dokar.

Ranar Alhamis din makon jiya ne 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da kudurin dokar.

A watan Mayu ne kasar ta yi fatali da dokar hana mata zubar a kuri'ar raba-gardamar da 'yan kasar suka kada.