Za a gurfanar da 'yan madigo a gaban kotun Kano

Dokar Najeriya ta haramta auren jinsi guda

Asalin hoton, PER-ANDERS PETTERSSON

Bayanan hoto,

A Najeriya akwai hukuncin dauri kan wanda aka kama da laifin auren jinsi guda

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce za ta kai wasu mata da ake zargi da madigo kotun shari'ar musulunci bayan an kama su suna shirin bikin aure a tsakanin su.

Mataimakin kwamandan Hisbah na jihar Isa Sani ya shaida wa BBC cewa sauran wadanda za a kai kotun sun hada da mutane 10 wadanda suka halarci wurin da aka shirya bikin, da kuma wanda ya bayar da hayar gidan da aka shirya bikin.

A ranar Litini ce hukumar ta damke matan a unguwar Sabon Garin Kano, kuma har yanzu hukmar na rike da guda biyu daga cikin su.

Mai magana da yawun kotun shari'a ta Kano, Baba Jibo Ibrahim ya ce suna sane da mmaganar sannan su na jiran hukumar Hisbah ta kawo maganar gaban kotun domin a fara sauraron karar.

Hukumar Hisbah ta ce za ta tuhumi matan ne da aikata rashin da'a, kasancewar ta kama su ne kafin a daura auren.

Dokar Najeriya dai ta haramta auren jinsi guda, kuma duk wanda aka kama da laifin zai iya kwashe kimanin shekara 14 a gidan yari.