Mata su bar kara gashi - Shugaban Museveni

Adebakyo tace tana yawo da gashin ta na asali mafi yawancin lokaci

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Abenakyo tace tana yawo da gashin ta na asali mafi yawancin lokaci

Shugaban Uganda Yoweri Museveni, ya yi tsokaci ga 'yar kasar wacce ta lashe kambin sarauniyar kyau ta duniya a kan karin gashi.

Shugaban ya wallafa wani hoto sarauniyar kyawun Quinn Abenakyo a shafinsa na Twitter, inda ya ce ''Dole ne mu nuna kyawun Nahiyar Afirka kamar yadda yake.''

An tambayi abun da yake nufi da karin ''gashin Indiya'', sai jami'i mai hulda da jama'a na kasar Don Wanyama ya bayyana wa BBC cewa " Kalli hoton za ka ga irin gashin dake kanta"

"Ba gashin kanta na asali bane. Yana nufin cewa ta bar gashin kanta "na gaskiya."

Asalin hoton, KAGIUTA MUSEVENI

Bayanan hoto,

Shugaba Museveni tare da Sarauniyar Kyau Quinn Abenakyo

Quinn Abenakyo ta bayyana cewa ta amince da ra'ayin Museveni a kan cewa "Kada a kwaikwayi shigar kasashen yamma."

"Abun ya rabu gida biyu ne a gare ni, yana da alaka da wurin da na ke da yanayin da nake ciki."

"Bai kamata wani ya yi iko da irin gashin da zaka sanya ba, idan ni ina son ai shi ke nan."