Uwar da ta je bankwana da danta mai cutar ajali

Wannan mai yiwuwa shi ne mafi munin tafiya da Shaima Swileh daga Yemen za ta taba yi a rayuwarta.

Ta je Amurka don yin bankwana da danta mai shekara biyu wanda yake cutar ajali.

A halin yanzu, Abdullah Hassan na rayuwa ne da tallafin na'urorin asibiti a California. Amma an hana mahaifiyarsa, Shaima Swileh shiga Amurka a karkashin wata doka da ta haramtawa 'yan wasu kasashen musulmi damar shiga kasar.

An bata takardun shiga Amurka bayan da ta samu gagarumin goyon baya daga jama'a, wadda zai bata damar yiwa danta bankwana.