Mutum 6 sun mutu a hatsarin jirgin sama

A na sa ran za a yi zabe a kasar ne ran 30 ga Disamba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A na sa ran za a yi zabe a kasar ne ran 30 ga Disamba

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mutane 6 ne suka mutu a wani hatsarin jirgin sama da ya faru a ranar Alhamis a Kinshasa.

Jirgin wanda hukumar zabe ta Congo tayi hayarsa ya fadi ne kusa da filin sauka da tashin jiragen sama dake Babban birnin kasar.

Rahoton ya bayyana cewa jirgin ya kai kayan zabe Tshikapa ne, inda a kan hanyarsa ta dawowa Kinshasa yayi hatsari.

Duka mutum 6 dake cikin jirgin sun mutu.

Sai dai hukumar zaben kasar ta shaida wa BBC cewa babu kayan zaben da su ka lalace a hatsarin.

A kwanakin baya ne dai ofishin hukumar zaben Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da ke Kinshasa babban birnin kasar ya kama da wuta.

Haka kuma an yi ta-ho-mu-gama da 'yan sanda a wuraren taron siyasa, inda mutane da dama suka mutu.