Raheem Sterling: 'Yan sanda na bincike zargin batanci

Raheem Sterling ne wanda aka nuna wa wariyar
Bayanan hoto,

Raheem Sterling ne wanda aka nuna wa wariyar

Jami'an 'yan sanda sun gana da wani mutum a tsanake bayan nuna wariyar launin fata da aka yi wa Raheem Sterling a lokacin da Chelsea ta doke Manchester City.

Abun dai ya faru da dan shekara 24 din ne a lokacin da aka ci City din 2-0 a Stamford Bridge a ranar 8 ga watan Disamba.

'Yan sanda a Birtaniya na duba bidiyo na kamarar tsaro domin dubawa ko an aikata laifin.

Sun samu bayanan dukkanin wadanda ake zargin suna da hannu a ciki, amma kawo yanzu ba su kama kowa ba.

Kungiyar Chelsea ta dakatar da mutum hudu daga halartar wasanninta a yayin da ake gudanar da bincike.

Kungiyar ta bayyana cewa tana ''goyon bayan 'yan sanda dari bisa dari.

Ta kara da cewa idan aka tabbatar da zargin nuna wariyar launin fata za su yi ''tsananin hukunci, ko ma kora.''