Majalisar Dinkin Duniya ta amince da yarjejeniyar yakin Hodeidah

Pro-government forces in Hudaydah

Asalin hoton, AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ta aika da tawagar da za ta sanya ido a kan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a birnin Hudaydah mai tashar jirgin ruwa.

Yarjejeniyar ta fara aiki ne tun ranar Talata bayan da wakilan bangarorin suka cimma matsaya a wata ganawa da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya.

Birtaniya ce ta shirya daftarin na Majalisar Dinkin Duniya, irinsa na farko cikin shekara uku a riricin na Yemen.

Za a tura tawagar Majalisar Dinkin Duniya su yi aikin sa ido a kan yarjejeniyar na wata guda.

Hudaydah birni ne mai nisan kilomita 140 yamma da Sanaa, babban birnin Yemen, kuma shi ne birni na hudu a girma a fagen kasuwanci kafin 'yan tawaye suka kwace shi daga gwamnatin kasar a 2014.