'Za mu yaki kungiyar IS' - al-Shabaab

al Shabaab fighters inside Somalia

Asalin hoton, AFP

Kungiyar al-Shabaab ta kasar Somaliya ta ce za ta yaki kungiyar IS da ke cikin kasar.

Kakakin kungiyar Sheikh Ali Rage ne ya bayyana haka a cikin wata hira da ya fitar, inda ya yi kira ga mayakan kungiyar al-Shabaab su kai hare-hare 'har sai sun shafe mayakan IS daga kasar'.

Duk da yake bangarorin biyu sun sha gwabza fada a wasu sassa na Somaliya a watannin baya bayan nan, wannan ne karo na farko da al-Shabaab ta fitar da irin wannan jawabin.

Kakakin kungiyar al-Shabaab ya saki sako na sautin muryarsa mai tsawon minti 42 a shafukan kungiyar na sada zumunta.

Kakakin kungiyar Sheikh Ali Rage ya zargi kungiyar IS da "kawo cikas ga yakin jihadin da ake yi a Somaliya".

Ya kuma kira kungiyar ta IS a matsayin "wata muguwar cuta" kuma "cutar daji", kuma ya kira mayakan al-Shabaab da su yaki kungiyar ta IS a kasar.

Da alama wadannan kalaman na mayar da martani ne ga ikirarin da IS ta yi cewa mayakanta sun kashe wasu mayakan al Shabaab a yankin Puntland.

Kungiyoyin biyu sun sha gwabza fada tun bayan da IS ta bayyana a Somaliya, inda ta kafa sansanoninta a arewacin kasar, kuma ta fara karbar kudin kariya daga 'yan kasuwan kasar, kamar yadda rahotanni daga kafafen watsa labarai suka ruwaito.