Karya ne - gwamnatinmu ba ta wani yaki da rashawa - Naja'atu

Hajiya Naj'atu Mohammed

Asalin hoton, TWITTER / AishaMBuhari

Bayanan hoto,

Hajiya Naj'atu Mohammed

Wata fitacciyar 'yar siyasa kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki, Hajiya Naja'atu Mohammed ta ce babu gaskiya cikin yaki da gwamnatinsu ke yi da cin hanci da rashawa.

Hajiya Naja'atu Muhammad daya daga cikin wadanda suka rika tallata Muhammadu Buhari a zaben 2015 ta shaida wa BBC cewa ba wani yaki da rashawa da gwamnatinsu ke yi.

"Mutum nawa aka kama, wasan kwaikwayo ne kawai ake yi," in ji ta.

Sai dai kuma a cikin jawabinsa na gabatar da kasafin kudi a zauren majalisa, shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu nasarori a yaki da cin hanci da rashawa, kuma nan ba da jimawa ba 'yan kasar za su ci moriyar kudaden da aka kwato.

Hajiya Naja'atu Muhammad 'yar siyasa daga jihar Kano ta yi tsokaci ne game da wasu jerin bidiyon da aka wallafa da ke zargin gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje na karbar kudaden da aka ce cin hanci ne daga hannun 'yan kwangila.

Ta kalubalanci gwamnatin tasu a kan rashin gudanar da bincike kan lamarin, duk da ikirarin da ta ke yi cewa tana yaki da rashawa.

"Idan zargi ne, me ya sa ba a yi bincike ba? Ai, idan ba a yi zargi ba, ba za a yi bincike ba. Idan ba a yi bincike ba, ai ba za a gano gaskiya ba."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ta ce a iyakar saninta, kotu ba ta isa ta hana 'yan sanda bincike ba.

A cewarta da ma ta san majalisar dokokin jihar Kano ba da gaske take yi ba wajen gudanar da binciken lamarin, don kuwa 'yan sanda ne suke da hakkin yin bincike.

Tun da farko, majalisar dokokin Kano ta kafa kwamiti don gudanar da bincike kan lamarin sai dai wata kotu ta dakatar da ita inda ta ce ba ta da hurumi.

Hajiya Naja'atu ta ce ba daidai ba ne hukumar EFCC ta juya baya a kan wannan batu, don kuwa ita da 'yan sanda suna da ikon su yi bincike don tabbatarwa ko wanke zargin da ake yi.

Ta ce ita ba ta yarda ba satar da dukiyar jama'a ba, ko daga wacce jam'iyya yake.

"Maciji duk maciji ne, kowanne ne daga PDP yake ko daga APC, zai yi sara ne ya cutar da mutane. Azzalumi, azzalumi ne. Kunama ce idan za ta harbe ki, ko wacce irin tuta ta dauka, sunanta kunama. Kisa za ta yi!

"Ni a ce an bar wani saboda kawai yana APC, ni wannan ban yarda da shi ba. Saboda an zalunci, zalunci ne."