Solskjaer ya fara ci wa Manchester United kwallaye biyar

Asalin hoton, Getty Images
Karon farko da Manchester United ta ci kwallaye biyar tun zamanin Ferguson
Ole Gunnar Solskjaer ya fara zamaninsa inda Manchester United lallasa Cardiff City 5-1, kungiyar da ya taba horar wa a gasar Firimiya ta Ingila.
Wannan ne wasan farko da Manchester United da ke matsayi na shida a teburin Firimiya ta buga, bayan sallamar Jose Mourinho.
Hankali yanzu ya koma ne ga sabon kocin na rikon kwarya domin ganin dubarun da zai bi wajen farfado da Manchester United.
Kocin ya samar da sauyi inda ya fara wasa da Phil Jones da Anthony Martial da Luke Shaw da kuma Pogba inda ya ajiye Eric Bailly da Romelu Lukaku da Diogo Dalot da kuma Matteo Darmian.
Zabin 'yan wasan kuma ya kawo sauyi a Manchester United inda ta ci kwallaye biyar a karon farko tun zamanin Sir alex Ferguson.
Ole ya taba aikin har da Cardiff na tsawon watanni takwas, inda ya gaza ceton kungiyar daga ficewa gasar Firimiya a 2014.
Ole ya ce ya koyi darasi daga kalubalen da ya fuskanta a baya a zamanin da yana Cardiff.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Manchester United dai da magoya bayanta na fatan ganin sauyi bayan sallamar Mourinho.
Tazarar maki 19 Liverpool ta ba Manchester United a teburin Firimiya. Kuma Manchester ta fi kusa da kasan tebur fiye da saman teburin gasar.
Da dama na ganin tsohon gwarzon kocin kungiyar, Sir Alex Ferguson ne ya yi uwa ya yi makarbiya wajen ganin an ba tsohon dan wasan na Manchester mai shekara 45 jan ragamar kulob di.
Ko da yake wasu na ganin Solskjaer mutum ne da ya cika kirki kuma ba lallai ne yana da zafi irin na Ferguson ba wanda kan kwada wa 'yan wasansa kira don su sauya taku idan wuri ya yi wuri.
Amma Sabon kocin na rikon kwarya, ya ce a bar ganinsa yana da sanyi, yana da zafi sosai.
Solskjaer dai tsohon dan wasan Manchester United ne da ya taba ci wa kungiyar kwallo mafi muhimmaci a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a 1999.
Ana ganin ya san sirrin kungiyar da kuma bukatunta don haka ake kulub din ke fatan zai iya kawo sauyi.