Al Shebaab na yaki da IS a Somalia

Mayakan Al Shebaab

Asalin hoton, AFP

Kungiyar Al-Shabaab ta ayyana kaddamar da yaki da kungiyar IS da ke da'awar jihadi a duniya.

Kakakin kungiyar Sheikh Ali Rage ne ya bayyana haka a cikin wani sakon murya da ya fitar a madadin kungiyar, inda aka ji shi yana kira ga mayakan kungiyar Al-Shabaab su kai hare-hare har sai sun fatattaki 'yan IS daga fadin Somalia.

Wannan ne karon farko da Al-Shabaab ta fitar da irin wannan jawabin, duk da cewa bangarorin biyu sun sha gwabza fada da juna a Somalia.

Al Shebaab ta zargi IS da dagula mata lamurra a yakin da take na tabbatar da jihadi a Somalia.

Bangarorin biyu sun shiga fada da juna ne tun shigar kungiyar IS a Somalia a 2015.

Yanzu ba a san tasirin wannan barazanar yaki ba tsakanin Shebaab da IS da kuma yakin da kungiyar ke yi da dakarun wanzar da tsaro na Afirka da kuma Somalia.

Kungiyar Shebaab ta dade tana kai hare-hare a Mogadishu a yakin da take domin hambarar da gwamnatin Somalia.

A 2011 ne aka fatattaki kungiyar daga Mogadishu, amma kuma ta ci gaba da zama barazana a wasu sassan kasar inda ta kashe daruruwan mutane tare da tursasawa dubbai gudun hijira.