Abubuwan da aka tattauna a taron ECOWAS a Abuja

Taron ECOWAS a Abuja

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rikicin siyasar Togo na cikin batutuwan da suka mamaye taron

Shugabannin kasashen Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, wato ECOWAS sun gudanar da wani taron yini daya a Abuja.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron wanda shi ne na 54 inda aka tattauna batutuwan da suka shafi yankin na yammacin Afirka.

Wasu batutuwa da taron ya mayar da hankali a kai sun hada da batun samar da kudin bai-daya tsakanin kasashen yankin.

Taron ya mayar da hankali kuma kan yaki da ta'addanci da rikicin siyasa a kasashen Togo da Guinea Bissau.

An dai shafe fiye da shekara daya, Togo na fama da rikicin siyasa tun watan Agustan 2017 inda masu zanga-zanga suka mamaye titunan kasar kan bukatar sauya dokar zabe.

Shugabannin kasashen na ECOWAS sun dauki mataki game da rikicin na Togo musamman bayan kammala zabe a ranar Alhamis.

Sun amince a ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin siyasar kasar.

Taron dai na zuwa mako daya bayan taron da aka gudanar a Abuja na shugabannin kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi.

A wajen taron Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da takwaransa na Chadi Idris Deby da Mahamadou Issoufou na Nijar da kuma Paul Biya na Kamaru sun amince da tsarin wasu bukatu guda takwas domin kawo karshen yaki da kungiyar Boko Haram da ta addababi yankin.