Likitoci sun shiga zanga-zanga a Sudan

demonstration in Atbara on 20 Dec

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Tashin hankalin ya shiga rana ta biyar a fadin kasar

Sabon rikici ya sake barkewa a Sudan yayin da lilitocin kasar sunka ce za su fara yajin aiki domin kara matsa wa Shugaba al-Bashir ya sauka.

Wata kungiya mai zaman kanta ta likitoci ta ce daga Laraba za mambobinta za su mayar da hankali ne kawai ga duba wadanda aka ji ma rauni ne kawai.

Ranar Asabar wani jagoran babbar jam'iyyar adawa ta kasar ya ce jami'an tsaro sun kashe masu zanga-zanga 22. Amma hukumomi sun ce wadanda aka kashe basu kai haka ba.

Rikici ya barke ne ranar Laraba da ta gabata bayan da gwamnati ta bayyana sabbin farashin biredi da man fetur.

A shekarar da ta gabata, farashin wasu kayayyaki ya nunka, kuma hauhawar farashi ya kai kusan kashi 70 cikin 100, kuma darajar kudin Sudan wato Jinai ta fadi warwas, kuma an rika samun karancin kayayyaki a manyan biranen kasar har da Khartoum.

Yadda rikicin ya samo asali

Rikicin ya fara ne a garin Atbara, inda masu zanga-zanga suka kona ofishin jam'iyya mai mulki ta National Congress Party.

A ranar Alhamis ,utum shida sun rasa rayukansu a zanga-zangar da ta auku a garin al-Qadarif da wasu mutum biyu kuma a Atbara.

Shaidu sun ce a wasu yankunan sojojin kasar sun shiga cikin masu zanga-zangar maimakon dakatar da su.

Wani mai ba shugaban kasar shawara, Faisal Hassan Ibrahim ya ce biyu cikin wadanda aka kashe a al-Qadarif sojojin kasar ne sanye da kayan gida. Ya kuma ce akwai wasu kungiyoyi da ke shirya jerin zanga-zangar da ke faruwa, amma bai bayyana ko su wane ne ba.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wannan hoton na nuna al-Bashir tare da shugaban Syria Assad a farko wannan wata a lokacin da ya ka wata ziyara can

Rikicin ya bazu zuwa birnin Khartoum da Omdurman da ma wasu sassan babban birnin kasar.

Ranar Asabar kuma kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wasu shaidu na cewa an kona ofisoshin jam'iyya mai mulkin kasar ta NCP a El Rahad yayin da masu zanga-zangar ke kira ga Mista Bashir ya sauka daga mukaminsa.

Kuma masu zanga-zanga sun rika daga murya mai karfi suna cewa "bamu yarda da rayuwa da yunwa ba" a Wad Madani, inda jami'an tsaro suka fesa masu hayaki mai sa hawaye.

Dalilin da ya sa tattalin arzikin Sudan ya shiga mummunan hali

Amurka ta dade tana zargin Shugaba al-Bashir da mara wa 'yan ta'adda baya a shekarun 1990, kuma an kakaba wa Sudan takunkumin karya tattain arziki.

A 2011 yankin kudancin kasar ya balle, inda ya tafi da kashi daya cikin uku na albarkatun man fetur na kasar. Wannan ya biyo bayan yakin basasr kasar da ya lankwame rayukan mutum miliyan 1.5.

Sannan rikicin da aka dade ana yi a yankin Darfur da ke yammacin kasar ya yi sanadiyyar raba mutum miliyan biyu da muhallansu bayan halaka fiye da mutum 200,00 da yayi.

An dage takunkumin da Amurka ta saka wa kasar a 2017, amma ba a sami wani cigaba ba tun lokacin.

A watan Janairun wannan shekarar an sami tashin hankali a Khartoum da wasu yankuna saboda tashin farashin biredi.

A shekarar 2016 Mista Bashir ya sanar da BBC cewa zai sauka daga mukamin shugaban kasar a shekarar 2020.