Hotunan abin da ya faru a sassan duniya daga 15 - 21 ga Disamba 2018

Mun zabo muku wasu hotuna masu kayatarwa na abin da ya faru a wasu sassa na duniya a makon da ya gabata.

A diver feeds a stingray while dressed as Santa Claus

Asalin hoton, EDGAR SU/REUTERS

Bayanan hoto,

Wani mutum mai suna Zhao Jian Wen sanye da kayan 'Father Christmas' ke ciyar da wani kifin Stingray a Singapore

Asalin hoton, Dan Kitwood/Getty Images

Bayanan hoto,

Dubban matafiya sun kasa isa garuruwansu bayan da aka rufe filin jirgin sama na Gatwick da ke Ingila saboda jami'ai sun ga wasu na'urori marasa matuki da ake sarrafawa daga nesa suna shawage a cikin filin jirgin. 'Yan sanda sun ce lamarin wani yunkuri ne na dagula ayyuka a filin jirgin "da gangar".

Asalin hoton, Goran Tomasevic/REUTERS

Bayanan hoto,

Wannan wata uwace da ke jimamin mutuwar danta da cutar Ebola ta kashe, a lokacin da ake binne shi a Beni dake cikin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Asalin hoton, MICHAEL DANTAS/AFP

Bayanan hoto,

Mazauna garin Manaus na kasar Brazil ke duba barnar da wata gobara ta yi wa unguwarsu ta Educandos. Babu wanda ya rasa ransa a wannan gobarar, amma ana ganin wani abin girki ne sanadin iftila'in.

Asalin hoton, Susana Vera/REUTERS

Bayanan hoto,

Nan kuma ma'aikata ke aikin hada wani mutum-mutumi da aka sanya wa suna Julia wanda mai yin mutum-mutumi dan kasar Spaniya, Jaume Plensa ya hada a birnin Madrid.

Asalin hoton, Zohra Bensemra/REUTERS

Bayanan hoto,

Wani dan kasuwa a kan titin Dakar babban birnin Senegal ya baje kolin kayan kawata gida don bikin Kirsimeti.

Asalin hoton, Shamil Zhumatov/REUTERS

Bayanan hoto,

Jami'ai masu aikin ceto ke isa wurin wani kumbo samfurin Soyuz MS-09 da ke dauke 'yan sama jannati da suka sauko daga tashar kasa da kasa a sasarin samaniya bayan kumbon ya sauka a wani yanki mai nisan gaske, wanda kuma kusa da garin Zhezkazgan na kasar Kazakhstan.

Asalin hoton, Matt Cardy/Getty Images

Bayanan hoto,

A nan masu sha'awar zane-zane ne ke daukan hoton wani sabon zane da shahararen mai zane Banksy yayi a garin Port Talbot na kasar Wales. Mista Banksy dan Birtaniya ne amma bai bayyana sunansa ba, sai dai ya tabbatar da cewa shi ne yayi wannan zanen a shafinsa na Instagram.

Asalin hoton, Obama Foundation/Chuck Kennedy/AFP

Bayanan hoto,

Nan kuma tsohon shugaban Amurka Barack Obama ne ke raba wa yara ma su jinya kyaututtuka a babban asibitin yara kanana da ke birnin Washington DC na Amurka.

Asalin hoton, Hannah McKay/REUTERS

Bayanan hoto,

Sai kuma wannan hoton na wasu yara da ke shirye-shiryen bikin Kirsimeti, ina anan suke rera wakokin yabo a cocin St Paul's Cathedral na birnin Landan.

Dukkan hotunan akwai hakkin mallaka a kansu.