An kulle dan jarida a India saboda Facebook

Wangkhem ya soki Babban ministan Manipur ne da Jam'iyyar BJP

Asalin hoton, FACEBOOK

Bayanan hoto,

Wangkhem ya soki Babban ministan Manipur ne da Jam'iyyar BJP

'Yan sanda sun yi wa gidan wani dan jarida dirar mikaya a Manipur mai iyaka da kasar Myanmar.

Sun kai samamen ne a gidan dan jaridar bane hawa biyu a ranar 27 ga watan Nuwamba.

'Yan sandan sun gaya wa dan jaridar Kishorecchandra Wangkhem, mai shekara 39, cewa shugaban 'yan sanda na son yin magana da shi.

"Babu abun da zai faru da kai, kada ka damu," Matar Wangkhem, Ranjita Elangbam, ta tuna wani 'dan sanda ya gaya masu.

Wangkhem na shirin watsa ruwa ne inda a bayan nan za su ci abincin rana tare da 'ya'yansa guda biyu, 'yar shekara biyar da yar shekara daya. Ya nemi da su bar shi ya kira lauyansa inda suka ki.

Sun ki amincewa da hakan inda suka ce masa da ya shirya su tafi a cikin minti biyar.

Matar shi da dan uwanta sun bi su a baya a cikin wata mota daban.

Bayanan hoto,

Ana zanga-zanga kan tsare Wangkhem

Bayan da suka isa ofishin 'yan sanda, sun jira na awa biyar a yayin da 'yan sanda ke yi wa Bangkhem tambayoyi. Yayin da sanyi ya fara saukowa bayan faduwar rana, sai matarsa ta koma gida domin ta dauko kayan sanyi. Bayan ta dawo ne ake gaya mata cewa mijinta an tafi da shi gidan kaso da ke wajen babban birnin kasar mai suna Imphal.

Laifin Wangkhem dai shi ne wallafa wasu bidiyo guda hudu a ranar 19 ga watan Nuwamba inda yake sukar karamar hukumarsa da jam'iyyar BJP, Inda ya bayyana cewa babban ministan Manipur "yaron" Firaminista Nerandra Modi ne.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manipur wuri ne dake fama da masu tada 'kayar baya a India

Dokar tsaro ta jihar ta bayar da dama a tsare mutum wanda shi barazana ne ga doka da oda a jihar har zuwa shekara daya ba tare da an kai shi kotu ba.

Da wannan dokar ne jam'iyar BJP da ke mulkin kudancin India ta kama maza musulmi miliyan 160 a baya.

Masu adawa da dokar sun ce dokar na nuna banbanci kuma ta take hakkin bil adama.