Liverpool da Man City sun fi damar lashe Firimiya a bana - Pochettino

Pochettino na Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pochettino ya ce akwai sauran aiki sosai ga Tottenham

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce Liverpool da Manchester City sun fi damar lashe kofin firimiya a bana duk da nasarar da Tottenham ta samu a kan Everton a ranar lahadi.

Tottenham ta uku a tebur, ta lallasa Everton 6-2 a Goodison Park inda ta datse yawan makin da ke tsakaninta da City, bayan Crystal Palace ta samu sa'ar Guardiola a Etihad

Yanzu tazarar maki biyu yanzu tsakanin Tottenham da Manchester City, kuma maki shida tsakaninta da Liverpool da ke saman teburin Firimiya.

Pochettino ya bayyana cewa kungiyarsa tana da yiyuwar lashe kofin na Firimiya a karon farko tun bayan 1961.

Ya kara da cewa "Akwai sauran aiki sosai kafin mu shiga sahun wadanda gasar a bana ta zaba."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Spurs ba ta sake cin kofin Firimiya ba tun bayan da ta lashe kambin a 1961

Tottenham ta ci wasanta guda hudu da ta buga inda ta ba Chelsea ta hudu a teburin rata da maki biyar, da kuma Arsenal ta biyar a kan tebur.