Bikin Kirsimeti; 'Yesu' na Kirista ko na Musulmi?

  • Daga Emre Azizlerli
  • BBC
Wani bangare daga cikin bangarori da dama na Al Kur'ani da aka ambaci Yesu ko Annabi Isa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani bangare daga cikin bangarori da dama na Al Kur'ani da aka ambaci Yesu ko Annabi Isa

Shin ya ka gudanar da naka bikin kirismeti?

Tambayar da kullum ake yi min ke nan lokacin Kirsimeti tun zuwa na Birtaniya shekaru 21 da suka gabata.

Ina cewa Turkiyya kasa ce ta musulmai - don haka ranar 25 ga watan Disamba rana ce kamar kowacce rana.

Kana nufin babu Kirismeti?

Ba wai kawai a Tiurkiyya ba, da yawan mutanen duniya ba sa bikin Kirismeti.

Wasu na mamakin hakan, musamman kasashen yammaci inda suke tunanin cewa Kirismeti biki ne da ake gudanarwa a fadin duniya.

Amma Kirismeti biki ne na murnar haihuwar Yesu, da Kiristoci ke bautawa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kirismeti lokaci ne na kawata gidaje da fitilu na ado

Ba biki ba ne na Yahudawa da mabiya addinin Hindu ko Musulmi ba.

Akwai mutane da yawa a kasashen musulmi da ke gudanar da bukukuwa amma yana faruwa ne a lokacin Idi ba Kirismeti ba.

Sanin bambancin haka yana da muhimmanci, tare da sanin abubuwan da suka hada mu.

Jesus !! kana nufin Yesu?

Wannan shi ne abun mamakin.

A musulunci ba a bikin haihuwarsa, amma ana girmama shi.

Musulmai na matukar girmama Yesu na addinin kirista.

Asalin hoton, Unknown

Bayanan hoto,

Zanen Maryama mai tsarki da wani musulmi ya yi kamar yadda aka suffanta a cikin Al Kur'ani

Al Kur'ani mai tsarki Ya girmama Yesu a matsayin daya daga cikin mafi daraja wandda ya zo kafin Annabi Muhammadu SAW.

A gaskiya ma Yesu - ko Annabi Isa da ake kiransa a Larabci - an anbace shi a Kur'ani fiye da sunan Muhammadu.

Hakazalika, akwai mace daya da aka ambata a cikin Al Kur'ani mai tsarki.

Maryam, kana nufin Maryam?

Ita ce Mary, ko Maryam da larabci, wadda aka saukar da Surah saboda ita, aka bayar da labarin budurcinta da haihuwar da ta yi.

Amma a wurin haihuwarta a musulunci babu Yusuf da shehunnai kuma babu ciyawa.

Maryam ita kadai ta haihu a sahara, inda ta zauna gefen mataccen iccen dabino.

Cikin ikon Allah, nan take dabino ya nuna ya fado Allah ya ciyar da ita kuma korama ta fara gudana a kasan kafarta.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Labarin Maryam da haihuwar danta ba tare da namiji ba na cikin zukatan mutane a al'adu daban-daban a cikin shekaru aru-aru da suka wuce

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Haihuwar mace marar aure ya diga ayar tambaya kan mutuncinta.

Amma shi jaririn da aka haifa, Isa AS, sai ya yi magana a matsayin Annabin Allah.

Wannan mu'ujizar ta wanke mahaifiyarsa.

Wannan labarin nasara ce a kan zargi.

Annabin ruhi ne

Idan musulmai suka ambaci Annabi Isa, ana tunanin za su kara da "amicin Allah a gare sa" kamar yadda idan an ambaci Annabi Muhammad SAW.

Kuma wa kake tuanin zai zo kafin tashin kiyama domin ya tabbatar da adalci, a musulunci?

Annabi Isa ne tabbas, zuwansa na biyu da daukakarsa a littattafan musulunci ya wuce Kur'ani.

Wani Shehin malamin addinin Islama Al-Ghazali ya kira shi da sunan "Annabin ruhi."

Ibn Arabi ya yi rubutu game da shi a matsayin "Cika-makin tsarkakakku."

A kasashen musulmai, akwai yara da yawa masu suna Isa, da mata masu suna Maryam.

Shin za ka iya mamakin akwai wani gida na Kiristoci da suke kiran dansu Muhammad?

A musulunci Isa ba bako ba ne, saboda lokacin da musulunci ya zo a karni na bakwai, Kiristanci ya riga ya kafu a gabas ta tsakiya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kama mutun biyar kan zargin kokarin tayar da bam a San Petronio basilica a Italiya

Saboda wasu dalilai, ba a ambaci sunan Muhammad a littafi mai tsarki Injila (Bible) ba.

Musulunci ya girmama Annabi Isa, amma a karni na baya ana iya cewa mujami'u ba su saka wa wannan karamcin ba.

Suna nuna Annabin musulunci a wuta, yana shan azaba a wata drama a karni na 15 da aka nuna a cocin San Petronio a Bologna, kasar Italiya.

Ayyukan kirkira irin wadannan a kasashen Turai suna nuna kaskanci.

Zagaye na tara na wuta

Wani mai zane a Italiya, Giovani da Modena, da mawaki Donte ya harzuka, shi ya ya laka wa Annabi Muhammad sunan zagayen wuta guda tara a wani wasan barkwanci.

Littafin ya karfafa masu zane sosai a kasar Turai a karni na 18, inda suka dinga yin zane suna alakantawa da Annabi Muhammad a wuta.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Malaman addinin Islama sun halarci taruka a Cocin-cocin Italiya domin yin Allah wadai da hare-haren da aka kai.

Daga cikinsu kawai mai kalar ruwa na William Blake, wani fitacce a wake da zane.

A wata coci a Belgium, a kasan wani mumbari na karni na 17 ya nuna Annabin Islama ya duka a kasa gaban wasu mala'iku.

Wannan a yanzu ba shi ba ne ra'ayin cocin.

Lokaci ya canza, amma zamaninmu na yanzu ma yana da na shi barazanari, zargi da tsattsauran ra'ayi.

Zaman tattaunawa na addinai

A shekarar 2002, wasu masu tsananin kishin Islama sun shirya tayar da bom a cocin Bologna.

Tun wannan lokacin, hare-hare sun janyo rasa rayuka da yawa, sun yi hakan da sunan musulunci, wanda hakan ya janyo rabuwa tsakanin mutane a kasashen Turai da kasashen musulmai.

Neman sani game da Annabi Isa a Musulunci da martabarsa yana da muhimmanci a yanzu fiye da kowanne lokaci, ga musulmai da Kirista gaba daya.

Sanin abun da ya hada addinai a yanzu zai iya kawo karshen rabuwa.