SERAP ta kai Bukola Saraki Kotu kan albashin Sanata Dariye

Sanata Bukola Saraki

Asalin hoton, SARAKI/FACEBOOK

Bayanan hoto,

Saraki na son takarda a hukumance game da hukuncin da aka yanke wa Sanata Dariye

Kungiyar SERAP, ta kai karar Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kotu, inda ta bukaci kotu ta tilasta ma shi dakatar da biyan tsohon gwamnan jahar Filato Sanata Joshua dariye albashi.

A bayanin da SERAP ta wallafa a shafinta na internet, ta ce ta shigar da karar ne a gaban wata babban kotun tarayya a Lagos don neman a tilasata wa Saraki dakatar da biyan Sanata Dariye albashi da alawus alawus, kasancewar yana tsare ne a gidan yari, kuma babu wani aikin majalisa da yake yi tun bayan tsare shi.

Daya daga cikin lauyoyin wannan kungiyar ta shaidawa BBC cewa, SERAP ta damu a kan cewa hukumar gudanarwa ta majalisar tarayya tana biyan Dariye albashin naira dubu 750, da kudaden alawus naira miliyan 13.5 a ko wane wata.

Sai dai a nata bangaren, majalisar dattijan Najeriya ta ce a halin da ake ciki babu wata doka da za ta dogara da ita wajen dakatar da biyan Joshuwa Dariye hakkokin da ake biyan takwarorinsa sanatoci.

Daya daga cikin masu taimaka wa shugaban majalisar dattawan a kan harkokin watsa labarai Mohammed Isa ya shaidawa BBC cewar, "har yanxu Dariye yana nan a matsayinsa na Sanata, har sai ministan shari'a ya rubutu wa majalisa takarda cewa an yanke wa Dariye hukuncin zama gidan kaso.''

Wannan yana nufin majalisar na son a sanar da ita ne hukumance game da hukuncin da aka yanke wa tsohon gwamnan.

A cikin watan Yulin bana ne wata kotu ta samu Sanata Dariye da laifin cin hanci da rashawa inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara 10.

A kwanakin baya ne dai kungiyar ta SERAP ta kai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Kara, inda kungiyar ta bukaci kotu ta tilasta wa shugaban da ya sa a binciki gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a kan zargi rashawa.